Dalilin da yasa muka yi Sallar Idi a ranar Asabar – Sheikh Lukuwa

Dalilin da yasa muka yi Sallar Idi a ranar Asabar – Sheikh Lukuwa

Wani malami a jihar Sokoto Sheikh Musa Lukuwa ya bayyana dalilin da yasa ya jagoranci wasu mutane suka gudanar da sallar Idi a ranar Asabar duk da cewa Sarkin Musulmi ya ce ranar Lahadi za ayi Sallar Idi.

A cewar Sultan, ba a gan jaririn watar Shawwal ba a Najeriya wadda hakan na nufin za a gudanar da azumin Ramadan 30.

A hirar wayar tarho da ya yi da wakilin Daily Trust, Lukuwa ya ce, "Sarkin Musulmi ya ce ba a ga wata ba amma mun ga watan saboda haka matsayar mu tafi ta shi."

A cewarsa, an ga jaririn watan a wurare da dama a Sokoto da wasu garuruwan da ke makwabtaka da jihar kuma an sanar da kwamitin sarkin musulmi amma ba su dauki mataki a kai ba.

Dalilin da yasa muka yi Sallar Idi a ranar Asabar – Sheikh Lukuwa
Dalilin da yasa muka yi Sallar Idi a ranar Asabar – Sheikh Lukuwa. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kwace kauyuka a Sokoto, sun nada sabbin alkalai - Sanata Gobir

Ya kara da cewa an samu sahihan rahoto da ke nuna cewa an ga jaririn watan a Yauri da Kamba a jihar Kebbi da kuma Zaria a jihar Kaduna har ma da Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da mu sunyi Sallar Idi a ranar Asabar.

"Wata dai daya ce kuma idan an gani a wuri daya ya isan ma dukkan musulmin duniya domin Manzon Allah SAW ya umurci musulmi su ajiye azumi idan an ga jaririn wata," in ji shi.

Lukuwa ya tuna lokacin da marigayi sarkin musulmi ya taba sanar da ganin wata misalin karfe 12 na rana, inda ya kara da cewa marigayi Sultan Ibrahim Dasuki da Muhammmadu Maccido ba su taba kin karbar ganin wata ba don karfe 7 na yamma ta wuce ko kuma don ya sabawa hasashen masana.

Da aka tuntube shi, Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin bayar da shawara a kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu sun yi biyaya ga dokar Sarkin Musulmi don shine zai iya fadar ranar da za ayi Idi.

Ya kara da cewa ya dauki wannan matakin ne a lokacin da ya samu sanarwar sarkin musulmin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164