COVID-19: An sallami mutum 90 da suka warke daga korona a Sokoto

COVID-19: An sallami mutum 90 da suka warke daga korona a Sokoto

Kawo yanzu, majinyata 90 ne aka sallama cikin wadanda suka kamu da coronavirus a jihar Sokoto kamar yadda shugaban kwamitin yaki da COVID-19 a jihar, Dr Ali Inname ya bayyana.

A halin yanzu akwai mutum 13 da ke jinyar cutar a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Inname wanda kuma shine kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana cewa an yi gwajin korona 617 a jihar inda sakamakon ya nuna 116 sun kamu yayin da cutar ta kashe mutum 13.

"Tsarin mu na 3Ts (nemo wandanda suka yi cudanya da masu cutar, yi musu gwaji da magani) yana bamu damar gano masu cutar kuma ayi musu magani bayan gwaji," in ji shi.

COVID-19: An sallami mutum 90 da suka warke daga korona a Sokoto
COVID-19: An sallami mutum 90 da suka warke daga korona a Sokoto. Hoto daga Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kwace kauyuka a Sokoto, sun nada sabbin alkalai - Sanata Gobir

Inname ya gwamnatin jihar Sokoto tare da hadin gwiwa da NCDC, WHO da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki ba dare ba rana domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Ya jadada bukatar musulmi suyi biyayya ga umurnin da Sarkin Musulmi, Mai Alfarma, Alh. Saad Muhammadu Abubakar da sauran masu ruwa da tsaki suka bayar na yin Idi a gidajensu don tsaron lafiya.

Ya kara da cewa, "Wannan ba lokaci bane na yin shagulgula ko ziyara, muna baku shawarar yin amfani da dandalin sada zumunta ko wasu hanyoyin wurin sada zumunci da yi wa juna murnar sallah.

"Amma a wurin da ziyarar ta zama dole sai a kiyayye dokar nesa nesa da juna, amfani da takunkunmi da amfani da hand sanitizer," a cewarsa.

Inname ya yi kira ga musulmi su yi amfani da wannan damar wurin yi wa jiharsu da kasa adduar Allah ya kawo karshen wannan annobar ta Covid-19.

A wani labarin, kun ji cewa hukumar gyaran hali ta jihar Kaduna ta ki karbar wani sabon fursuna da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta kawo mata.

Sanusi Danmusa, shugaban gidan gyaran halin, a ranar Jumaa ya ce an ki karbar sabon fursunan ne saboda kare wadanda ke gidan gyaran halin daga kamu da COVID-19.

Ya ce gidan gyaran halin ta dena karbar sabbin wadanda aka yanke wa hukunci har ma da masu ziyara saboda bullar annobar ta coronavirus.

An yanke wa Sadiq Musa, mai sanaar canjin kudi hukucin zaman shekaru bakwai a gidan gyaran hali ba tare da zabin biyan tara ba.

Da ya ke tsokaci a kan rashin karbar fursunan, shugaban hukumar EFCC na Kaduna, Yakubu Mailafia ya ce bai san inda hukumar gidan gyran halin ta ke so ya kai wanda aka yanke wa hukuncin ba.

Ya ce, "Hukumar EFCC tana da kaida game da tsare masu laifi kuma gidan gyaran hali shi ne wuri na karshe da ake kai wadanda aka yanke wa hukunci, ina za mu kai su?"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel