Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 135 a Katsina da Zamfara

Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 135 a Katsina da Zamfara

Rundunar sojin Operation Hadarin Daji ta tarwatsa sansanin 'yan bindiga tare da nasarar halaka a kalla 135 daga cikinsu.

Dakarun sojin saman sun kai samamen ne tsakanin ranar 22 zuwa 23 na watan Mayun 2020 a wurare da dama na maboyar 'yan bindigar da ke jihohin Katsina da Zamfara.

Daga cikin sabon salon kakkabe 'yan bindigar da suka gallabi jama'ar jihohin Katsina da Zamfara, gwamnatin tarayya ta kara tura dakarunta yankin.

A makon da ya gabata ne 'yan bindigar suka saka yankunan a gaba inda suke yi wa jama'a kisan kiyashi tare da kwashe musu Shanunsu.

Bayan kiran da shugabannin yankin tare da masu fadi a ji suka dinga yi wa gwamnatin tarayya, an tura karin sojoji da za su kawo karshen lamarin.

KU KARANTA: An damke malamin da ya yi wa El-Rufai 'wankin babban bargo' a kan hana sallar Idi

Hakazalika, sojin saman sun kai hari a sansanin Hassan Tagwaye da na Alhaji Auta tare da na Maikomi.

Shugaban dakarun sojin saman Najeriya ya jinjinawa rundunar Operation Hadarin Dajin a kan wannan gagarumar nasarar

Ya umarcesu da su dage wajen tabbatar da cimma manufar shugaban sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, na kakkabe 'yan bindigar tare da dawowar zaman lafiya yankin.

A wani labari na daban, Sheikh Bello yabo dan asalin jihar Sokoto ya shiga hannun jami'an tsaro tun bayan bazuwar bidiyon da ya caccaki gwamnan Kaduna a kan hana sallar Idi.

A wani sautin murya mai tsayin kusan minti biyar, malamin addinin Islama mai suna Sheikh Bello Yabo, ya caccaki Gwamna Malam Nasir El-Rufai saboda hana sallar Idi da yayi a jihar Kaduna.

A sautin muryar, ya yi kira ga Musulmi da su bijirewa hukumomi a kowanne gari da aka hana su fita sallar Idin karamar sallar don dakile yaduwar cutar korona, kamar yadda jaridar SaharaReporters ta ruwaito.

Malamin ya yi ikirarin cewa, gwamnan jihar Kaduna da duk takwarorinsa da suka hana sallar Idi ba korona suke yaka ba, Musulunci suke yaka.

Ya zargi gwamnan da bada kwanaki biyu tak don zuwa kasuwanci da siyayya amma ya hana zuwa Masallaci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: