Covid-19: Najeriya za ta fara sallamar masu cutar korona koda basu warke ba
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara sallamar masu cutar korona da wuri koda kuwa ba a tabbatar da sun warke ba.
Darakta janar din hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa, Chikwe Ihekweazu, ya sanar da hakan a yayin jawabi ga kwamitin yaki da annobar korona ta fadar shugaban kasa.
Ihekweazu ya ce wata alama ta bayyana cewa za a iya sallamar majinyatan cutar koda kuwa sakamakon gwajin bai bayyana cewa basu dauke da cutar ba. jaridar Premium Times ta ruwaito.

Asali: Twitter
"Sabuwar alama ta bayyana cewa koda mutum na dauke za a iya sallamarsa matukar an yi jinya na wani lokaci. Za a iya sallamar majinyatan su koma gida su yi jinya.
"A don haka, muna kallon wannan matakin kuma za mu iya sauya dokokinmu kowanne lokaci.
"Na fara sanar da hakan ne ta yadda zamu fara shirin karbar wasu sauye-sauye nan ba da dadewa ba," yace.
" Wannan hukuncin gwamnatin za a iya danganta shi da rashin cibiyoyin killacewa wadanda za su isa a fadin kasar nan."
A baya, Ihekweazu ya ce Najeriya bata da isassun wuraren killace masu cutar korona a jihohin kasar nan.
Ya ce gwamnatin tarayya na duban cewa ko za a fara jinyar cutar a gidaje ba tare da an garzaya asibiti ba.
"A fadin kasar nan, muna da gadaje 3,500 na jinyar korona amma a jihar Legas muna kokarin samar da kari.
"A don haka muna kokarin samar da karin gadaje," Ihekweazu yace.
A ranar 20 ga watan Mayu, mutum 6677 ne aka tabbatar da suna dauke da cutar korona a Najeriya. Duk da an sallama mutum 1840 ne suka warke aka sallamesu, an rasa rayuka 200.
A wani labarin kuma, ministan sadarwa na Najeriya, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yaba wa wasu gwamnonin kasar da suka karbi sabon kudirin saukaka tsadar sadarwa wanda ake kira Right of Way Resolution (RoW).
A ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu, Ministan cikin wata sanarwa da sa hannun hadiminsa na sadarwar zamani, Dr Femi Adeluyi, ya bayyana farin ciki a kan kokarin da gwamnonin suka yi na amincewa da sabon kudirin na RoW.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng