Pantami ya yabi gwamnonin da suka karbi kudirin rage kudin sadarwa na RoW

Pantami ya yabi gwamnonin da suka karbi kudirin rage kudin sadarwa na RoW

Ministan sadarwa na Najeriya, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yaba wa wasu gwamnonin kasar da suka karbi sabon kudirin saukaka tsadar sadarwa wanda ake kira Right of Way Resolution (RoW).

A ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu, Ministan cikin wata sanarwa da sa hannun hadiminsa na sadarwar zamani, Dr Femi Adeluyi, ya bayyana farin ciki a kan kokarin da gwamnonin suka yi na amincewa da sabon kudirin na RoW.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta tunatar, kungiyar gwamnonin Najeriya a ranar 22 ga watan Janairun 2020, ta amince da kawo karshen matsalar da ake fuskanta ta tsadar hanyoyin sadarwa na fasahar zamani.

Kungiyar gwamnonin ta amince da kudirin ne da manufar bunkasa yawan arzikin Najeriya (GDP) ta hanyoyin sadarwar masu amfani da fasahar zamani.

Gwamnonin sun amince da sabon kudirin RoW, wanda majalisar tattalin arzikin Najeriya ta kaddamar tun a shekarar 2013.

Majalisar tattalin arzikin kasar ta kayyade farashin N145 a kan kowane mizani 1 na wayar sadarwa da ake kira Fibre optics.

Ministan Sadarwa; Dr Isa Ali Ibrahim Pantami
Ministan Sadarwa; Dr Isa Ali Ibrahim Pantami
Asali: Twitter

A yayin rungumar wannan sabon kudiri hannu biyu-biyu, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a ranar 20 ga watan Mayu, ya rattaba hannu kan dokar rage tsadar farashin mita daya ta Fibre Optics ga kamfanonin sadarwa a jiharsa daga N4,500 zuwa N145 kacal.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya za ta mayar da yaki da cutar korona a hannun Gwamnoni

Gwamnan Imo ya yi koyi ne da takwaransa na jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, wanda tun a ranar 12 ga watan Mayu, ya shigar da kudirin cikin dokar jiharsa.

Haka kuma, gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i da na Katsina; Aminu Bello Masari gami da na jihar Filato; Simon Bako Lalong, sun karbi wannan sabon kudiri inda tuni suka sanya shi cikin doka a jihohinsu.

A sanadiyar haka Ministan shugaba Muhammadu Buhari na ma'aikatar sadarwa, Sheikh Pantami, ya bayyana farin ciki tare da yabawa gwamnonin biyar da suka yi wannan yunkuri da zai bunkasa yawan arzikin Najeriya.

Yayin da Ministan yake yaba wa gwamnonin biyar, ya nemi sauran gwamnonin kasar da su dabbaka wannan doka da za ta taka rawar gani wajen bunkasa ci gaban kasa musamman a fannin ilimin sadarwa na fasahar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel