COVID-19: Sabbin mutum 339 sun kamu, 28 a Kano, 22 a Katsina, jimilla ya haura 7,000

COVID-19: Sabbin mutum 339 sun kamu, 28 a Kano, 22 a Katsina, jimilla ya haura 7,000

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 339 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.48 na daren ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 339 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

139-Lagos

28-Kano

28-Oyo

25-Edo

22-Katsina

18-Kaduna

14-Jigawa

13-Yobe

13-Plateau

11-FCT

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnonin Arewa sun nemi tallafin kudi wurin Buhari

8-Gombe

5-Ogun

4-Bauchi

4-Nasarawa

3-Delta

2-Ondo

1-Rivers

1-Adamawa

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar 21 ga watan Mayun 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 7016.

An sallami mutum 1,907 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 211.

A wani rahoton, kun ji cewa iyalan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar’adua sun bayar da gudunmawar kayan abinci da kayan kare kai daga kamuwa da kwayoyin cuta, PPE, ga hukumar kula da Abuja, FCTA.

Sun bayar da kayayyakin ne a matsayin gudunmawarsu wurin yaki da annobar coronavirus da ta adabi kasashen duniya ciki har da Najeriya.

An bayar da tallafin ne karkashin gidauniyar iyalin mai suna Women and Youth Empowerment Foundation (WYEF).

Kayayyakin da gidauniyar ta bayar sun hada da takunkumi 1,000, sabulu 1,800, katon din makaroni 100, buhannan semolina 100, buhannan shinkafa 100, hodar wanki leda 23,100 da takunkumin likitoci 13,000.

Yayin mika kayayakin ga FCTA, wakilin iyalan, Malam Abdullahi Umaru Yar’adua, ya yaba da jajircewa da sadaukar da kai da ma'aikatan lafiya ke yi wurin dakile yaduwar cutar.

Mallam Yar’adua ya ce, "Gidauniyar mu ta WYEF da ni kai na muka mika godiyar mu ga gwamnatin tarayyar Najeriya, kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan COVID-19, Kwamitin bayar da shawara kan COVID-19 na Abuja da duk wadanda ke aiki don yaki da annobar a kasar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel