An ci gaba da musayar yawu tsakanin Amurka da China kan sakacin bullar annobar korona

An ci gaba da musayar yawu tsakanin Amurka da China kan sakacin bullar annobar korona

Musayar yawu ta yi zafi gami da nuna yatsa a tsakanin kasar Amurka da China, dangane da surkullen da suka mamaye yanayin da ya haddasa bullar cutar korona a duniya.

Gwamnatin Amurka na ci gaba da zargi da nuna yatsa a kan China, da cewar ita ta yi duk wani ruwa da tsakin da ya janyo yaduwar annobar korona a sassan duniya.

Sai dai gwamnatin China ta mayar martani tare da yi wa Amurka raddi da cewa, ba ta jin dadin wannan zargi da ta misalta a matsayin kazafi.

A ranar Alhamis ne dai gwamnatin China ta yi wa shugaban Amurka, Donald Trump, martani da cewa, ta yi iyaka bakin kokarinta wajen tseratar da rayukan mutane yayin da cutar ta bulla karo na farko.

Ta kuma ce har a yanzu ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da jajircewa a kan ganin cutar ta zama tarihi.

Da yake ganawa da manema labarai, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar China, Zhao Lijian, ya ce babu wani kokari da suke a halin yanzu face tseratar da rayuka da lafiyar al'umma.

A nasa bangaren, cikin wata sanarwa da shugaban Amurka ya fitar ya ce, duk masu ikirarin cewa sakacin da kasar China ta yi ba shi ya haifar da annobar korona ba a duniya, to kuwa sun kasance sakarkaru.

Donald Trump da Shugaban kasar China; Xi Jinping
Donald Trump da Shugaban kasar China; Xi Jinping
Asali: Instagram

Sakon da Mista Trump ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, yayin jaddada sakacin da China ta yi, ya yi amfani da kalmar 'Wacko' wadda a turance take nufin marasa hankali.

Yana mai cewa, wasu marasa hankali a kasar China su na ganin cewa gwamnatinsu ba ta da laifi a kan barkewar annobar korona alhali kuwa duk rayukan da suka salwanta a fadin duniya sanadiyar cutar sun rataya a wuyanta ne.

KARANTA KUMA: Labari mai dadi: WHO ta nuna goyon baya a kan maganin cutar korona na kasar Madagascar

Haka kuma sashen Hausa na BBC ya ruwaito Trump yana cewa, kasar China na da ikon hana yaduwar cutar zuwa sauran sassan duniya, illa dai kawai tana da wata manufa a kan hakan.

A hakan ne dai shugaban na Amurka ya ce tabbas sai an gudanar da gagarumin bincike domin gano matakan da gwamnatin China ta dauka tun a yayin da cutar korona ta fara bulla a kasar.

Mista Trump bai gushe ba dai yana ci gaba da cewa, kamata ya yi a ce gwamnatin China ta dauki matakai cikin hanzari na hana annobar korona bazuwa daga tushenta.

Babu shakka dai annobar coronavirus ta kashe dubban mutane a fadin duniya, tun bayan bullar bakuwar cutar mai shafar numfashi a watan Disamban 2019 cikin garin Wuhan na kasar China.

Babu tantama a baya Mista Trump ya sha kiran cutar korona ''Yar China'. Sakatarensa na harkokin waje Mike Pompeo, yana kira cutar ''Yar Wuhan', abin da ke matukar bata wa gwamnatin China rai.

Trump da sakatarensa sun yi tir da gwamnatin China kan saken da ta yi a kan barkewar cutar tun fil azal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel