Rashin tsaro: Sama da mutane 500 aka kashe a jihohi 10 cikin watanni 3

Rashin tsaro: Sama da mutane 500 aka kashe a jihohi 10 cikin watanni 3

A yayin da a baya-bayan nan matsalar rashin tsaro ta sake tabarbarewa a fadin kasar nan musamman Arewacin Najeriya, wani bincike ya nuna rayukan fiye da mutum 500 sun salwanta a cikin watanni uku kacal.

Binciken manema labarai na jaridar Daily Trust ya gano cewa, rashin tsaro ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 500 cikin wasu jihohi 10 na Najeriya a tsawon watanni uku da shude.

Mutanen da rayukansu suka salwanta sun hadar da fararen hula, jami'an tsaro da kuma 'yan sa-kai a sanadiyar rikici kabilanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma tayar da kayar baya.

Yankunan kasar da wannan mummunan lamari ya dugunzuma sun kasance yankin Arewa ta Tsakiya, Arewa ta Gabas, da kuma Arewa ta Yamma.

Jihohin 10 da suke neman zaman lafiya da kwanciyar hankali ruwa a jallo sun hadar da; Katsina, Kaduna, Taraba, Zamfara, Niger, Benue, Sokoto, Borno, Yobe da kuma Adamawa.

Shugaba Buhari yayin ganawa da shugabannin tsaro na Najeriya
Shugaba Buhari yayin ganawa da shugabannin tsaro na Najeriya
Asali: Facebook

Wannan lamari wani dori ne a kan wahalhalu da matsi na tattalin arziki da ke fuskantar miliyoyin mutane a yankunan a yayin da annobar cutar korona ta ke ci gaba da tsananta.

KARANTA KUMA: Babu ranar sassauta dokar kulle a jihar Kaduna - El-Rufa'i

Ana ci gaba da samun banbance-banbance na tunkarar wannan mummunan lamari a tsakanin gwamnoni da jami'an tsaro a yankunan da zaman lafiya ya dade da yin layar zana.

Sai dai ko shakka babu al'umma da mazauna yankunan wanda su kadai suka san irin hatsarin da suke ciki, babu abin da suke bukata a halin yanzu face rokon a kawo musu dauki kafin wataran a waye gari babu su gaba daya a doron kasa.

Dubban dangi sun rasa 'yan uwa da makusanta a yayin da ba dare ba rana rashin tsaro yake ci gaba da kara yawan zawarawa da kuma marayu, wanda hakan yake kara tsananta katutu na talauci da sauran kalubale na rayuwa.

Haka kuma wani hasashe ya nuna sakamakon rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, kimanin mutane 8, 000 sun kwanta dama a shekaru goman da suka gabata.

Kungiyar ICR ta bayyana cewa, bayan mutane 8, 000 da su ka rasa rayuwakansu a dalilin rashin tsaro a yankin, an tarwatsa mutane fiye da 260, 000 daga mahallansu a wannan lokaci.

A rahoton da kungiyar mai suna International Crisis Group ta fitar kwanan nan a shafinta na yanar gizo, ta ce jihar Zamfara ce gaba wajen fama da matsalar rashin tsaro.

Kungiyar mai zaman kan-ta ta ce wadannan mutane da aka fatattaka su na gudun hijira. Daga cikin wadanda aka raba da gidajensu, akwai mutum 60, 000 da suka fake a kasar Nijar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel