Yanzu-yanzu: Ana gobara a Hedkwatar NIPOST dake Abuja

Yanzu-yanzu: Ana gobara a Hedkwatar NIPOST dake Abuja

Mumunar gobara ya auku a hedkwatar hukumar ayyukan aika da karban sako watau NIPOST dake birnin tarayya Abuja.

Rahoton TheCable ya bayyana cewa gobarar ta fara ci ne tun karfe 9 na safiyar ranar Laraba, 20 ga May, 2020.

An samu labarin cewa ma'aikata da yawa na cikin ofishin lokacin da wutar ta fara ci amma daga baya jami'an kwana-kwana sun samu nasarar kashe wutar.

Wannan shine karo na biyar da manyan ofishohin gwamnatin tarayya a Abuja ke gobara duk da cewa maaikata na zaune a gidajensu.

An umurci maaikatan gwamnati suyi zamansu a gida saboda dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta sanya a Abuja.

KU KARANTA: Kar ka bari a yi Sallar Idi a Kaduna - Sheikh Gumi ya aikawa El-Rufa'i sako

Idan baku manta ba, a ranar 21 ga Afrilu, anyi gobara a ofishin babban bankin Najeriya CBN, reshen Jos, jihar Plateau.

Bayan haka, ranar 17 ga Afrilu, hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja ta ci bal-bal kuma anyi asarar dukiyoyin gwamnati.

Kuma dai, ranar Larabar, 14 ga watan Afrilu 2020, gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.

Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.

Hakazalika a makonni kafin gobarar CAC, gobara ta lashe ofishin akawunta janar na tarayya wacce akafi sani da baitul malin gwamnati dake Abuja.

Bayan gobarar ta kwashe lokaci tana ci bal-bal karamin ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, Prince Clem Agba, ya yi magana a kan gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel