A fara neman wata ranar Juma'a amma da wuya a gani - Sarkin Musulmi

A fara neman wata ranar Juma'a amma da wuya a gani - Sarkin Musulmi

Shugaban Majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya NSCIA kuma Sarkin Musulmi, Alh Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni ya yi kira yan Musulmai su nemi watar Shawwal ranan Juma'a.

Mai Alfarman ya bayyana hakan ne a jawabin da Majalisar NSCIA ta saki ranar Litinin inda yayi wasu bayanai game rashin yiwuwan ganin watan amma dai kawai a nema.

Ya bayyana cewa Musulman Najeriya su saurari sanarwarsa domin sanin ranan karewar watar Ramadanan bana.

Jawabin yace: "Bisa ga shawaran kwamitin neman wata, ranar Juma'a, 22 ga Mayu, 2020 wanda yayi daidai da 29 ga Ramadana 1441AH ne ranar fara neman watan Shawwal 1441AH."

"Amma a ranar, watan zai fito yan mintuna kadan kafin rana ya fadi wanda hakan ke nufin ganin watan ba zai yiwu ba."

"Amma dai, shugaba, bisa ga sunnar Manzon Allah (SAW) ya yi kira ga al'ummar Musulmi su nemi watar Shawwal 1441AH bayan faduwar ranar Juma'ar."

"Ana kira ga dukkan Musulman Najeriya su saurari sanarwar mai alfarma, shugaban NSCIA, kan karewan watar Ramadana."

KU KARANTA: Daya daga cikin mambobin FCC 37 da Buhari ya nada ya mutu kafin rantsar da su

Bayan haka, kwamitin neman watan tarayya ta raba wani faifan bidiyon wani matashi a Tuwita inda yake bayani kan rashin yiwuwar ganin wata ranar Juma'a.

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel