Korona: Sabbin mutane 338 sun karu a Najeriya, mutane 64 a Kano

Korona: Sabbin mutane 338 sun karu a Najeriya, mutane 64 a Kano

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 338 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin 11:20 na daren Lahadi a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

177-Lagos

64-Kano

21-FCT

16-Rivers

14-Plateau

11-Oyo

9-Katsina

4-Jigawa

4-Kaduna

3-Abia

3-Bauchi

3-Borno

2-Gombe

2-Akwa Ibom

2-Delta

1-Ondo

1-Kebbi

1-Sokoto

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:10 na daren ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 5959 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 1594 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 182.

DUBA WANNAN: An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

A ranar Asabar ne ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da mutuwar karin mutane biyu da suka kamu da cutar korona.

Ma'aikatar ta sanar da haka ne a sanannen shafinta na tuwita.

"Ya zuwa karfe 11:55 na daren ranar 16 ga watan Mayu, an samu karin mutane biyu da cutar korona ta kashe, yayin da aka sallami karin wasu mutanen biyu daga cibiyar killacewa.

"Jimillar mutanen da aka sallama ya zuwa yanzu sun kai 93, babu wanda ya kamu da cutar a yau, Asabar," a cewar sanarwar.

Sai dai, alkaluman NCDC sun gusar da duk wani karfin gwuiwa da jama'ar Kano su ka fara samu dangane da lafawar da su ka fara tunanin annobar ta yi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel