Rikicin kabilanci: Rayuka 48 sun salwanta a jihar Adamawa (Hotuna)

Rikicin kabilanci: Rayuka 48 sun salwanta a jihar Adamawa (Hotuna)

A kalla mutum 48 ne aka kashe a rikicin kabilanci da ya auku a karamar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa.

Ana shirya gawawwakin da aka kashe sakamakon rikicin don yi musu jana'iza baki daya duk da kuwa ana tsammanin kara samun wasu gawawwakin, wata majiya ta sanar da SaharaReporters a ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi amfani da miyagun makamai a yayin rikicin a Tigno da ke karamar hukumar Lamurde.

An samu rashin rayuka masu tarin yawa da dukiyoyi.

SaharaReporters ta gano cewa, rikicin ya barke ne a daren Alhamis tsakanin asalin 'yan kabilar Chobok da kuma Hausawa, kamar yadda majiya daga yankin ta sanar.

An gano cewa, rikicin ya barke ne sakamakon fadan da ake yi na yanka Alade a mayankar garin. Daga nan ne aka fara fadan da ya janyo kashe-kashe.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma bai bada yawan jama'ar da suka rasa ransu ba.

Ya ce, "Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bai wa kwamandan kwantar da tarzoma tare da kwamandan yankin Numan umarnin cewa dukkan DPO da ke yankin su fada aiki."

Rikicin kabilanci: Rayuka 48 sun salwanta a jihar Adamawa (Hotuna)
Rikicin kabilanci: Rayuka 48 sun salwanta a jihar Adamawa (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kashe-kashen Katsina: FG ta dauka mataki mai tsauri

Rikicin kabilanci: Rayuka 48 sun salwanta a jihar Adamawa (Hotuna)
Rikicin kabilanci: Rayuka 48 sun salwanta a jihar Adamawa (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

A wani labari na daban, a yau Asabar 16 ga watan Mayun 2020, gwamnatin tarayya ta tura dakarunta don yaki da 'yan ta'addan da suka gallabi jihar Katsina.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa, Gwamna Aminu Bello Masari ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da aka yi da shi a wani gidan rediyo a Katsina.

Masari ya ce dakarun sojin daga jihar da gwamnatin tarayya za a tura su sassan jihar ne don yaki da ta'addanci.

A yayin tattaunawa da gwamnan, ya jaddada cewa duk kalubalen tsaron ana kan shawo kansu, amma gwamnatin tarayya ce ke bada umarnin komai don ita ce mai rundunar sojin.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar ta samar da makamai da dukkan kayan aikin da sojin ke bukata don yaki da 'yan ta'addan.

Bincike ya nuna cewa, kananan hukumomi shida na jihar na cikin tashin hankali sakamakon harin da 'yan bindigar ke kai musu kullu yaumin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel