Yan bindiga suna samun daurin gindi daga wajen manyan mutane a Neja – Gwamna Bello

Yan bindiga suna samun daurin gindi daga wajen manyan mutane a Neja – Gwamna Bello

Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa akwai wasu manyan mutane a jahar dake baiwa yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane bayanan sirri.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito kimanin kananan hukumomi 5 yan bindiga suka addaba da suka hada da Rafi, Shiroro, Mariga, Lapai da kuma Munya.

KU KARANTA: Gwamnan jahar Zamfara ya yi wasu muhimman nade nade guda 4 a gwamnatinsa

Yan bindigan sun kashe jama’a, sun sace na sacewa sa’annan sun lalata dimbin dukiyoyi na miliyoyin nairori, tare da sabbaba dubunnan mutane yin gudun hijira.

Kakaakin gwamnan, Mary Noel-Berje ce ta sanar da haka a ranar Alhamis, inda tace wannan zagon kasan shi ne abin da yasa hukumomin tsaro basu samun galaba a kan miyagun.

Yan bindiga suna samun daurin gindi daga wajen manyan mutane a Neja – Gwamna Bello
Gwamna Bello Hoto: ThisDaylive
Asali: UGC

“Wannan ba karamin matsala bane, saboda yan bindigan suna aiki ne tare da wasu manyan mutane a garuruwan da ake kai harin, su ke basu bayanan sirri, da haka suke tsallake tarko da jami’an tsaro ke sanya musu.” Inji ta.

Don haka gwamnan ya nemi jama’a su taimaka ma gwamnati a yakin da take yi da miyagun yan bindiga ta hanyar kai rahoton duk wanda suka sani yana aiki da yan bindigan.

Haka zalika gwamnan ya bayyana girman fadin kasar jahar da girman dazukanta a matsayin wani kalubale da hukumomin tsaro suke fuskanta, saboda a dazukan yan bindiga suke fakewa.

“Ina tabbatar muku da cewa muna iya kokarinmu don tabbatar da mun samar da ingantacce tsaro ga jama’anmu, zamu nasara ne a kan miyagu idan muna samun bayanan sirri game da ayyukansu, don haka muke bukatar taimakon kowa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, mayakan ta’addanci ta ISWAP su 11 sun mika wuya ga dakarun Soji na Operation Lafiya Dole a jahar Adamawa sakamakon matsin lamba da suke fuskanta daga Sojoji.

Shugaban sashin watsa labaru na shelkwatar, Manjo Janar Enenche ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu.

A cewar Enenche ko a ranar 10 ga watan Mayu sai da yan Boko Haram suka jibge iyalansu mutum 72 a daidai kofar shiga karamar hukumar Ngala da misalin karfe 8:30 na dare.

A yanzu haka da mayakan ISWAP 11, da iyalan yan Boko Haram din duk suna hannu, kuma za’a dauki matakan da suka dace akan su.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel