Kyauta muka samu maganin cutar korona na kasar Madagascar - Boss Mustapha

Kyauta muka samu maganin cutar korona na kasar Madagascar - Boss Mustapha

Sabanin rahotannin da ake yadawa, gwamnatin tarayya ta ce ba ita ta nemi a kawo mata maganin korona na kasar Madagascar ba.

Gwamnatin Najeriya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ta ce shugaban kasar Madagascar ne ya aiko da mata da maganin gargajiyar kyauta ba tare da kashe ko sisin kobo ba.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana da fadar shugaban kasa ta kafa don yaki da cutar a Najeriya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja.

Sanarwar Sakataren Gwamnatin ta zo ne a yayin zaman karin haske kashi na 31 kan halin da ake ciki dangane da cutar korona a kasar.

Boss Mustapha ya ce Gwamnatin Madagascar ta turo da maganin Najeriya kyauta kuma ba tare da an nemi bukatar hakan ba.

A baya bayan nan an yi ta rade-radin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a kwaso wa Najeriya maganin da kasar Madagascar ta sarrafa wanda ake ikirarin yana da tasiri wajen warkar da cutar.

Har ila yau dai Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta na nan dai a kan bakanta na cewa kawo yanzu ba a samu wani maganin cutar korona ba, saboda haka mutane su daina amfani da maganin da ba shi da tabbas.

Hakan ya sanya WHO ta yi watsi da ikirarin da shugaban Madagascar ya yi na cewa maganin gargajiya da aka samar a kasarsa na iya warkar da masu cutar sarkewar numfashi ta korona.

Kasar Madagascar dai wani tsibiri ne a tsakiyar tekun Indiya da ke da nisan kilomita 400 daga gabashin Afirka, al’ummar kasar sun kai miliyan 26 tun kidayar da aka gudanar a shekarar 2018.

Sai dai duk da wannan gargadi na Hukumar Lafiya ta Duniya, wasu kasashen Afirka kamar su Tanzania da Guinea-BIssau, tuni sun karbi wannan magani hannu biyu-biyu.

Kasashen baya ga bayyana farin cikinsu da kuma alfahari da kasar Madagascar, sun yi amanna da yadda maganin ke yakar cutar korona.

Madagascar ta binciko wannan magani na gargajiya daga wani ganye wanda ta sarrafa shi kamar ganyen shayi, kuma ta sanya masa suna COVID-Organics.

Maganin cutar korona na kasar Madagascar: Covid-Organics Hakkin mallakar hoto: Aljazeera
Maganin cutar korona na kasar Madagascar: Covid-Organics Hakkin mallakar hoto: Aljazeera
Asali: Twitter

A ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun 2020, shugaban kasar Andry Rajoelina ya kaddamar da maganin, wanda suke amfani da shi wajen magance cutar ta Covid-19.

Maganin COVID-Organics ya warkar da mutane 92 daga cikin mutum 128 da suka kamu da cutar a kasar, 36 suka rage, kuma ba’a samu koda mutum daya da ya mutu sakamakon cutar ba.

KARANTA KUMA: Yanzu amfani da takunkumin rufe fuska ya zama tilas - Gwamnatin Tarayya

A zahiri dai wannan magani yana dauke da sunadarin artemisia, wanda akasari ake amfani da shi don maganin zazzabin cizon sauro, kuma Cibiyar bincike ta kasar ita ce ta binciko maganin.

Duk da tasirin wannan maganin a kasar Madagascar na warkar da masu cutar korona, Hukumar Lafiyar na ci gaba da jaddada cewa, maganin bai samu tabbacin masana kimiyya ba saboda haka bai inganta ba.

Sai dai ko shakka babu, wannan ra'ayi ya sha ban-ban da shugaban Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo da takwaransa na Tanzania, John Magufuli, inda tuni suka bazama wajen shigo da maganin kasashensu.

Shugabannin biyu sun ce lallai al'ummominsu za su ci gaba da ribatar wannan magani domin magance cutar korona wadda ta zamto alakakai a fadin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel