Filla-filla: Jerin wurare 25 da ake gwajin Coronavirus a Najeriya, 11 ke Arewa

Filla-filla: Jerin wurare 25 da ake gwajin Coronavirus a Najeriya, 11 ke Arewa

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da samun wajen gwajin cutar Coronavirus na 25 a fadin tarayya da kuma jihohin da layin samun dakin gwaji.

NCDC ta bayyana hakan ne ranar Juma'a, 15 ga watan Mayu, 2020 a shafinta na Tuwita.

Jawabin yace: "Muna farin cikin sanar da samin wajen gwajin cutar Coronavirus na 25 a fadin tarayya wato Asibitin tarayya dake Yola, jihar Adamawa."

"Wadanda ake shirin samarwa yanzu sune a jihohin: Katsina, Kwara, Anambara da Gombe."

Legit.ng ta kawo muku jerin wurare 25 dake jihohin Najeriya da ake gwaji yanzu:

1. Jihar Sokoto (Wuri 1)

2. Jihar Kano (Wurare 3)

3. Jihar Kaduna (Wurare 2)

4. Birnin tarayya Abuja (Wurare 2)

5. Jihar Plateau (Wuri 1)

6. Jihar Borno(Wuri 1)

7. Jihar Adamawa (Wuri 1)

8. Jihar Oyo (Wuri 1)

9. Jihar Osun (Wuri 1)

10. Jihar Ogun (Wuri 1)

11. JiharLegas (Wurare 4)

12. Jihar Edo (Wurare 2)

13. Jihar Delta (Wuri 1)

14. Jihar Imo (Wuri 1)

15. Jihar Rivers (Wurare 2)

16. Jihar Ebonyi (Wuri 1)

A bangare guda, Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 193 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 12 na safiyar ranar Jumaa, 13 ga watan Mayun na shekarar 2020.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 12:00 ranar Jumaa, 15 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 5,162 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar Covid-19 a fadin Najeriya.

An sallami mutane 1180 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 167.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel