Yanzu-yanzu: Mutane 5 sun halaka yayinda sabon Rikici ya barke tsakanin kabilu biyu a jihar Adamawa

Yanzu-yanzu: Mutane 5 sun halaka yayinda sabon Rikici ya barke tsakanin kabilu biyu a jihar Adamawa

Hukumar 'yan sandan Najeriya, shiyar jihar Adamawa, Arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da labarin ɓarkewar rikicin tsakanin wasu kabilu biyu a garin Tinno, karamar hukumar Lamorde na jihar.

Rahoton ya bayyana cewa an samu barkewar rikicin ne tsakanin Hausawa mazauna garin da kabilar Chobo, kuma ana tsoron cewa mutane da dama sun halaka.

BBC ta ruwaito daga wasu mazauna garin cewa wani dan karamin saɓani aka samu sakamakon buge wani ɗan ƙabilar Chobo da wani matashi bahaushe yayi.

Saboda haka `yan uwan wanda aka kade da babur suka far ma mai babur ɗin, inda wasu kuma daban sukayi kokarin kare shi, kawai sai rikici ya yi kamari.

Wani mazaunin garin, Sulaiman Bello, ya shaida cewa "Muna cikin mawuyacin hali saboda yanzu an yi mana ƙawanya ko ta ina kana jin ƙarar bindigogi kawai."

Wani majiyan daban ya bayyanawa PremiumTimes cewa: "Rikicin ya fara ne da safiyar Juma'a kuma har zuwa karfe 3 na rana ana cabawa. Za ka iya jin karan bindiga yanzu haka da muke magana."

"Yanzu haka mun kirga gawawwakin mutane biyar kuma babu jami'an tsaro har yanzu a wajen."

Domin tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Yahaya Nugroje, ya bayyana cewa su ma yanzu ne suke tattara bayanai kan ainihin abin da ya faru.

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin kabilu biyu a jihar Adamawa
Yan sanda a Adamawa Hoto: Titi
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kalli sabon faifan bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan yan Boko Haram a Borno

A wani labarin daban, Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da samar da wajen gwajin cutar Coronavirus a jihar Adamawa wanda shine na 25 a fadin tarayya da kuma jihohin da layin samun dakin gwaji.

Jawabin yace: "Muna farin cikin sanar da samin wajen gwajin cutar Coronavirus na 25 a fadin tarayya wato Asibitin tarayya dake Yola, jihar Adamawa."

Legit.ng ta kawo muku jerin wurare 25 dake jihohin Najeriya da ake gwaji yanzu:

Karanta a nan Filla-filla: Jerin wurare 25 da ake gwajin Coronavirus a Najeriya, 11 ke Arewa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel