Coronavirus: Almajirai 35 sun warke a Kaduna

Coronavirus: Almajirai 35 sun warke a Kaduna

Gwamnati jihar Kaduna ta sake sallamar karin almajirai 35 wanda a baya sakamakon gwaji ya nuna cewa su na dauke da kwayoyin cutar korona.

Channels TV ta ruwaito cewa, Kwamishinan lafiya ta jihar, Dr Aminu Baloni, ita ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis da daddare.

Dr Baloni ta bayyana cewa, an sallami almajiran daga cibiyar killace masu cutar korona ta jihar bayan sun warke.

A cewar kwamishinan, an sallami almajiran ne bayan sun kammala jinya kuma sakamakon gwaji har sau biyu ya tabbatar ba sa dauke da kwayoyin cutar.

Ta ce a yanzu haka jihar Kaduna tana da mutum 47 masu cutar, inda aka samu asarar rayuka hudu yayin da an sallami mutane 63 bayan sun murmure.

A wani rahoton mai nasaba da wannan, gwamnatin jihar Kano ta sanar da killace daliban Almajirai 2000 domin takaita yaduwar cutar korona a jihar.

Coronavirus: Almajirai 35 sun warke a Kaduna
Coronavirus: Almajirai 35 sun warke a Kaduna
Asali: Twitter

Rahoton ya bayyana cewa kwamishanan lafiyan jihar, Aminu Tsanyawa, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da horon ma'aikatan da za'a daurawa nauyin kula da yaran a cibiyoyin killace masu cutar.

KARANTA KUMA: Mutane 'yan shekaru 31 zuwa 40 sun fi saurin kamuwa da cutar korona - NCDC

Ya ce wadanda ake horaswa sun hada da Likitoci, ma'aikatan jinya, da masu gwajin da zasu gwada dukkan yaran.

A cewarsa, an ajiye wadannan Almajirai ne a sansanin killacewa uku a kananan hukumomin Kiru, Gabasawa da Karaye.

A yanzu, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana cewa jihar Kano ta mutane 707 da suka kamu da cutar ta Coronavirus.

Yayin da aka sallami 79 bayan sun samu lafiya, 33 sun rigamu gidan gaskiya.

Alkaluman da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka NCDC ta fitar a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayu, sun nuna cewa cutar korona ta harbi mutum 5,162 a duk fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel