COVID-19: An kama mutum 155 da suka saba dokar kulle a Sokoto

COVID-19: An kama mutum 155 da suka saba dokar kulle a Sokoto

Rundunar Yan sanda ta jihar Sokoto ta kama mutum 155 daga karfe 8 na daren ranar Laraba zuwa karfe 6 na ranar Alhamis da suka saba dokar kulle da aka saka a jihar don dakile yaduwa annobar COVID-19.

Wannan na cikin wata sanarwa ce ta mai magana da yawun rundunar, Muhammad Sadiq, mai mukamin mataimakin superintendent na yan sanda ya fitar a ranar Alhamis a Sokoto kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mr Sadiq ya ce twagar hadin gwiwa ta jamian tsaro karkashin jagorancin kwamishinan Yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje, daga ranar 5 ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Mayu ta kama motoci da babura a kalla 63.

COVID-19: An kama mutum 155 da suka saba dokar kulle a Sokoto
COVID-19: An kama mutum 155 da suka saba dokar kulle a Sokoto. Hoto daga BBC
Asali: Facebook

DUBA WANNAN Satar shanu: Kansilar da ake nema ruwa a jallo ya shiga hannu

Ya ce, "An gudanar da ingattacen binciken a kan kamen da aka yi kamar yadda kwamishinan yan sanda ya bayar da umurni kafin a kai su kotu."

Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kama duk wani mutum ko kungiya ta aka samu da saba dokar ta hana fita.

"Ina kira ga alummar Sokoto su rika biyaya ga doka tare da bin shawarwarin da hukumomi suka bayar su rika zama a gidajen su da dadare domin an saka dokar ne saboda dakile yaduwar kwayar cutar a jihar."

A wani rahoton, kun ji cewa Wakana Enan Ngari, Kansilar da ake nema ruwa a jallo a kan zargin satar shanu da wasu laifufuka a jihar Adamawa ya mika kansa hannun Yan sanda a karamar hukumar Numan na jihar.

DSP Suleiman Nguroje, Mai magana da yawun rundunar yan sanda na Adamawa ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis a Yola kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Nguroje ya ce an tafi da kansilar da ake zargi zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar (CID) domin cigaba da bincike.

Nguroje ya ce, "Rundunar yan sandan jihar Adamawa tana son sanar da alumma cewa Kansila mai wakiltan mazabar Vulpi a karamar hukumar Numan ya mika kansa ga yan sanda."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel