Jigawa ta samu karin mutane 51 masu Coronavirus, 31 Almajirai ne

Jigawa ta samu karin mutane 51 masu Coronavirus, 31 Almajirai ne

Gwamnatin jihar Jigawa ta samu karin mutane 51 da suka kamu da muguwar cutar Coronavirus, 31 cikinsu Almajirai ne da aka turo daga jihar Kano.

Kwamishanan lafiyan jihar, wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19, Dakta Abba Zakari, ya tabbatar da hakan ne ga manema labarai a sansanin yan bautar kasa NYSC dake Dutse.

A cewarsa, kashi 56 cikin 100 na masu dauke da cutar Coronavirus a jihar Jigawa Almajirai ne da aka kawo daga jihar Kano.

Ya ce gwamnatin Badaru Talamiz na iyakan kokarinta wajen basu abinci, wajen kwana da wasu abubuwan da suke bukata.

Ya bayyana cewa daga cikin matakan da ake dauka a jihar son takaita yaduwar cutar a jihar ya hada wajabta sanya takunkunmin fuska, bada tazara, da kuma wanke hannu.

Baya ga hakan, kwamishanan ya ce za'a fara da gwajin mutane a jihar Jigawa saboda tuni sun sayi kayayyakin gwaji da za'ayi amfani da su a dakin binciken asibitin Dutse.

Yace: "Sabuwar dakin gwajin zai saukaka wahalan da ake sha wajen kai samfuri Abuja da Kaduna."

A yanzu, adadin masu dauke da cutar Coronavirus a jihar Jigawa ya kai 163 yayinda 3 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Gwamnan Gombe ya janye dokar hana Sallar Jam'i, ya ce a bude Masallatai

Jigawa ta samu karin mutane 51 masu Coronavirus, 31 Almajirai ne
Jigawa Hoto: Gwamna Badaru
Asali: Facebook

A bangare guda, Gwamnatin jihar Kano ta sanar da killace daliban makarantun allo da aka fi sani da Almajirai 2000 domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

Rahoton ya bayyana cewa kwamishanan lafiyan jihar, Aminu Tsanyawa, ya sanar da hakan ranar Alhamis a bikin kaddamar da horon ma'aikatan da za'a daurawa nauyin kula da yaran a cibiyoyin killacewan.

Ya ce wadanda ake horaswa sun hada da Likitoci, ma'aikatan jinya, da masu gwajin da zasu gwada dukkan yaran.

A cewarsa, an ajiye wadannan Almajirai ne a sansanin killacewa uku a kananan hukumomin Kiru, Gabasawa da Karaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel