Sojojin kasar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram 50 a Najeriya

Sojojin kasar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram 50 a Najeriya

Sojojin jamhuriyyar Nijar sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 75 a yankin tekun Chadi a wani atisaye mai taken Liwur.

'Yan ta'addar kungiyar Boko Haram sun kashe a kalla mutane 36,00 da suka hada da daruruwan mazauna Diffa, lamarin da ya sa gwamnatin kasae kaddamar da atisayen.

A cikin wani jawabi da ma'aikatar tsaro ta kasar Nijar ta fitar ranar Laraba, ta ce dakarunta sun kashe mayakan kungiyar 25 a kudancin jihar Diffa, babban birnin kudu maso gabashin kasar Nijar.

Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa dakarun sojin kasar sun kashe karin wasu mayakan kungiyar Boko Haram 50 a kasar Najeriya a wasu atisaye guda biyu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Rundunar sojojin jamhuriyar Nijar ta ce ta kwace mota daya, babura biyu da sauran wasu makamai masu yawa na amfanin sojoji daga hannun 'yan ta'addar.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Rundunar sojin Najeriya a karkashin atisayen OPSH a jihar Filato ta tabbatar da mutuwa wani matashi, Rinji Bala, mai shekaru 20, wanda ya ke aji uku a jami'ar Jos.

Sojojin kasar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram 50 a Najeriya
Sojojin kasar Nijar Hoto: AFP
Asali: UGC

A ranar Talata ne dakarun rundunar OPSH suka harbi Bala, wanda aka fi sani da 'Bobo', a ofishinsu da ke kan titin zuwa Zaria a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

DUBA WANNAN: Ba zan taba saduda ba, tsohon faifai ake yadawa - Shekau ya fitar da sabon sako

Da ya ke tabatarwa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) faruwar lamarin, kakakin rundunar OPSH, Ibrahim Shittu, ya ce basu ji dadin abinda ya faru ba.

A cewar Shittu, mai mukamin manjo a rundunar soji, jami'an rundunar OPSH sun samu kiran kar ta kwana a kan al'amuran wasu batagari, har ma suka kama matasa bakwai da ake zagi suna daga cikinsu.

Ya bayyana cewa daga baya sun sallami Bala da wasu sauran matasa hudu bayan sun gano cewa basu da laifi, amma a hanyarsu ta fita daga ofishin, sai wani soja ya yi kuskuren tunanin cewa guduwa zasu, lamarin da yasa ya bude musu wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel