Jihohi 35 a Najeriya wanda coronavirus ta bulla - NCDC

Jihohi 35 a Najeriya wanda coronavirus ta bulla - NCDC

Ya zuwa yanzu dai an samu bullar cutar korona a jihohi 35 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda kididdigar hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta tabbatar.

Tabbas mahukuntan lafiya na ci gaba fadi-tashi ba dare ba rana domin dakile yaduwar cutar korona a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa tamkar wutar daji.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Talata, 12 ga watan Mayun 2020, ta ce cutar korona ta harbi mutane 4,787 yayin da tuni an sallami mutum 959 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan da suka warke.

Jadawalin NCDC ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu dai cutar corona ta hallaka mutum 158 a fadin kasar.

Da misalin karfe 11.54 na ranar Talata da daddare, NCDC ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 146 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 146 da cutar ta harba cikin jihohin 20 sun kasance kamar haka: Lagos(57), Kano(27), Kwara(10), Edo(9), Bauchi(8), Yobe(7), Kebbi(4), Oyo(4), Katsina(3), Niger(3), Plateau(2), Borno(2), Benue(2), Sokoto(2), Gombe(1), Enugu(1), Ebonyi(1), Ogun(1), FCT(1), Rivers(1).

Har ila yau jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai kuma jihar Kano a mataki na biyu yayin da birnin tarayya Abuja ya biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos-1,990; Kano-693; Abuja-360; Ogun-127; Gombe-119; Osun-39; Katsina-208; Borno-188; Edo-88; Oyo-69; Kaduna-111; Bauchi-190; Akwa Ibom-17; Kwara-44; Sokoto-108; Ekiti-15; Ondo-16; Rivers-23; Delta-17; Taraba-17; Jigawa-118; Enugu-11; Niger-9; Abia-2; Zamfara-73; Benue-4; Anambra-1; Adamawa-21; Plateau-19; Imo-3; Bayelsa-6; Ebonyi-8; Kebbi-28; Nasarawa-25; Yobe-20.

Ga jerin adadin mutanen da cutar korona ta hallaka a jihohin Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos (33), Abuja (7), Kano (33), Ogun (5), Kaduna (3), Akwa Ibom (2), Katsina (11), Sokoto (13), Edo (4), Borno (16), Ebonyi (1), Osun (4), Oyo (2), Ekiti (1), Delta (3), Rivers (3), Nasarawa (1), Yobe (1), Zamfara (5), Jigawa (2), Ondo (1), Kebbi (3), Kwara (1), Gombe (1), Bauchi (3) .

Sannan kuma ga jerin adadin mutanen da suka warke a jihohin Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos (502), Kano (74), Abuja (65), Katsina(18), Ogun (46), Kaduna (17), Bauchi (23) Akwa Ibom (10), Kwara (9), Anambra (1), Edo (13), Ondo (11), Enugu (2), Osun (30), Oyo (16), Ekiti (9), Delta (3), Rivers (4), Sokoto (22), Neja (2), Plateau (1), Imo (1), Abia (1), Borno (12), Gombe (53), Jigawa (4), Zamfara (1), Kebbi (1), Taraba (1), Bayelsa (3).

An samu bullar cutar korona cikin dukkanin jihohin Najeriya in banda jihar Kogi da kuma Cross River.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel