Kano: Kotu ta bada umarnin damko shugaban karamar hukuma da ya yi rubda ciki a kan tallafi

Kano: Kotu ta bada umarnin damko shugaban karamar hukuma da ya yi rubda ciki a kan tallafi

Wata kotun majistare da ke zama a Kano ta bada umarnin damko Malam Kabiru Ado-Panshekara, shugaban karamar hukumar Kumbotso da ke jihar a kan kin bayyana a gaban kotu.

Alkalin kotun majistaren, Musa Ibrahim ya bada damar kamo wanda ake zargin don ya gurfana a gaban kotu sakamakon zarginsa da ake da cin amana.

Mai gurfanarwa, Salisu Tahir, ya sanar da kotun cewa a ranar 9 ga watan Mayun 2020, wanda ake zargi kuma shugaban karamar hukumar Kumbotso, an damka masa fom na raba tallafin rage radadi.

"Wanda ake zargin ya waskar da wasu fom din inda ya bai wa wasu wadanda basu cancanta ba," yace.

Tahir ya yi kira ga kotun da ta bada damar damko wanda ake zargin saboda ya ki zuwa kotun koda aka aika masa da sammaci.

Ya ce laifinsa ya ci karo da sashi na 315 na dokokin Penal Code da kuma sashi na 26 na dokokin rashawa na 2008, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Kano: Kotu ta bada umarnin damko shugaban karamar hukuma da ya yi rubda ciki a kan tallafi
Kano: Kotu ta bada umarnin damko shugaban karamar hukuma da ya yi rubda ciki a kan tallafi. Hoto daga The Nationn
Asali: Twitter

KU KARANTA: Magajin Abba Kyari: Rashin tabbacin da ke tattare da nadin farfesa Gambari

Lauyan wanda ke kare kansa, Ibrahim Adamu, ya sanar da kotun cewa bai san dalilin da ya hana wanda ake zargin gurfana a gaban kotun ba.

"Daya daga cikin hadiman Ado Panshekara ya sanar da ni cewa yana kan hanyar zuwa kotun," yace.

Adamu ya roki kotun da ta kara wa wanda ake zargin mintocin 30 don ya samu isowa.

Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 27 ga watan Mayu.

A wani labari na daban, cutar korona ta kashe Dr Kabir Tijjani, shugaban babban asibitin Mani da ke jihar Katsina.

Babban likitan ya rasu ne a ranar Talata kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta sanar wa SaharaReporters.

Majiyar ta ce an gano marigayin na dauke da muguwar cutar ne a makon da ya gabata kuma an mayar da shi daya daga cikin cibiyoyin killacewar da ke jihar.

A yammacin Talata, 12 ga watan Mayun 2020 kuwa babban likitan yace ga garinku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel