Allah mai iko: Yadda mai jinyar korona ta haihu a asibitin Najeriya

Allah mai iko: Yadda mai jinyar korona ta haihu a asibitin Najeriya

Wata mata mai shekaru 37 da ke fama da cutar korona ta haifa yaro Namiji a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas da ke Idi-Araba.

Hukumar asibitin ce ta sanar da hakan a wata takarda da ta bai wa manema labarai a ranar Talata.

Kamar yadda takardar ta bayyana, majinyaciyar korona din ta haifa yaro namiji a ranar Asabar da ta gabata.

Amma kuma, ba ta bayyana cewa ko jaririn yana dauke da muguwar cutar ba.

Takardar ta ce, "Kungiyar likitoci da ma'aikatan jinya sun karba haihuwar wata mata da ke dauke da cutar COVID-19. Ta haifa yaro namiji mai nauyin 2.6Kg.

"Matar mai shekaru 37 ta haihu ne bayan likitoci sun fede ta a ranar Asabar, 9 ga watan Mayu. Mahaifiyar da jaririn suna cikin koshin lafiya.

"Muna taya dukkan ma'aikatan lafiya da ke sahun gaba murnar wannan nasarar."

Wannan haihuwar an yi ta ne a yayin da ake tsaka da annobar korona a jihar Legas, jaridar The Punch ta ruwaito.

A ranar 11 ga watan Mayu, hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta ce jihar Legas na da mutum 1,933 da aka tabbatar suna dauke da cutar korona. 1,398 daga ciki har yanzu suna dauke da cutar, 502 sun warke sai 53 suka rasa rayukansu.

A ranar 27 ga watan Afirilu, wata majinyaciya mai shekaru 40 ta haifa yarinya mace a asibitin.

Allah mai iko: Yadda mai jinyar korona ta haihu a asibitin Najeriya
Allah mai iko: Yadda mai jinyar korona ta haihu a asibitin Najeriya. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: An rasa rayuka 6 bayan musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da dakarun soji

A kalla rayuka shida aka rasa bayan ruwan wutar da ya wanzu tsakanin sojoji da 'yan bindiga a wani kauyen da ke jihar Binuwai.

'Yan bindigar sun kai hari kauyen a daren Litinin da ke yankin Agasha ta karamar hukumar Guma da ke jihar.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa maharan sun shiga kauyukan da karfe 11:30 na dare inda suka fara harbe-harbe. Sun kashe mutum 2 tare da raunata wasu daban.

Ganau ba jiyau ba sun sanar da gidan talabijin din Channels cewa, an harbi wata tsohuwa da ke zama a kusa da makarantar firamare ta Agasha yayin harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel