COVID-19: Cutar korona ta kashe shugaban babban asibitin Katsina

COVID-19: Cutar korona ta kashe shugaban babban asibitin Katsina

- Allah ya yi wa Dr Kabir Tijjani, shugaban babban asibitin jihar Katsina da ke Mani, rasuwa

- Majiya daga iyalan mamacin ta bayyana cewa cutar korona ce ta kashe shi a ranar Talata

- An tabbatar da marigayin na dauke da muguwar cutar a makon da ya gabata kafin a mika shi cibiyar killacewa

Cutar korona ta kashe Dr Kabir Tijjani, shugaban babban asibitin Mani da ke jihar Katsina.

Babban likitan ya rasu ne a ranar Talata kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta sanar wa SaharaReporters.

Majiyar ta ce an gano marigayin na dauke da muguwar cutar ne a makon da ya gabata kuma an mayar da shi daya daga cikin cibiyoyin killacewar da ke jihar.

A yammacin Talata, 12 ga watan Mayun 2020 kuwa babban likitan yace ga garinku.

Tuni aka birne likitan karkashin tsauraran matakan da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bada a garin Katsina.

Kamar yadda hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta bayyana, jihar Katsina na da mutum 205 da aka tabbatar suna dauke da muguwar cutar.

COVID-19: Cutar korona ta kashe shugaban babban asibitin Katsina

COVID-19: Cutar korona ta kashe shugaban babban asibitin Katsina. Hoto daga SaharaReporters
Source: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

A wani labari na daban, jami'an 'yan sanda sun ceto wasu mata biyu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sace su a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Ya yi bayanin cewa sun yi nasarar ceto matan bayan kiran da suka samu a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

'Yan bindigan da za su kai 10 sun tsinkayi kauyen Sabon Layi a babura dauke da bindigogi kirar AK 47 inda suka yi awon gaba da matan.

"Daga nan ne DPO na karamar hukumar Kurfi ya jagoranci rundunar Operation Puff Adder da 'yan sa kai inda suka bi 'yan bindigar har kauyen Kaguwa sannan suka yi musayar wuta," takardar tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel