Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 146 sun kamu da Coronavirus, Legas da Kano a gaba
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 146 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:55 na yammacin ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 146 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;
57-Lagos, 27-Kano, 10-Kwara, 9-Edo, 8-Bauchi, 7-Yobe, 4-Kebbi, 4-Oyo, 3-Katsina, 3-Niger, 2-Plateau, 2-Borno, 2-Sokoto, 2-Benue, 1-Gombe, 1-Enugu, 1-Ebonyi, 1-Ogun, 1-FCT, 1-Rivers
A yau, an sallami mutane 57 bayan sun samu waraka kuma an yi rashin mutane 8.
KU KARANTA: Jerin Jihohin da su ka samu fiye da Jakada guda a sababbin nade-naden da aka yi
NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:55 na yammacin ranar Talata, 12 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4787 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.
An sallami mutane 959 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 158.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng