Sunayen jakadu 42 da Buhari ya ke neman majalisar dattawar ta amince da su
- Shugaba Buhari ya tura sunayen jakadu 42 zuwa majalisar dattawa
- Shugaban kasar ya nemi majalisar ta tabbatar tare da tantance su
- Sanata Ahmed Lawan ne ya karanta wasikar Buhari a zauren majalisar yayin zamanta na ranar Talata
A ranar Talata, 12 ga watan Mayu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tura wa majalisar dattawa ta Najeriya sunayen jakadu 42 da zai nada domin ta tantance su.

Asali: Facebook
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, shi ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da aka gudanar a yau.
A yayin zaman majalisar, Sanata Lawan ya karanta wasikar da shugaban kasar ya aiko musu mai dauke da kwanan watan ranar 6 ga Mayu, 2020.
KARANTA KUMA: Coronavirus: Sanatocin Najeriya sun saba dokar ba da tazara a zaman majalisa
A cewar Buhari, bukatarsa ta yi daidai da sashe na 171 (1), (2) (c) da sashi na (4) cikin kundin tsarin mulkin kasa da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 1999.
Ga jerin sunayen zababbun jakadun 42 da Buhari ya tura wa majalisar dattawa da kuma jihohin da suka fito:
- C.O. Nwachukwu (Abia);
- A. Kefas (Adamawa);
- R.U Brown (Akwa Ibom);
- G.A Odudigbo (Anambra);
- O.C Onowu (Anambra);
- Y.S. Suleiman (Bauchi);
- E.S. Agbana (Bayelsa);
- B.B.M. Okoyen (Bayelsa);
- G.M. Okoko (Benue);
- A.M. Garba (Borno);
- M.I. Bashir (Borno);
- M.O. Abam (Cross River);
- A.E. Allotey (Cross River);
- G. E. Edokpa (Edo);
- A. N. Madubuike (Enugu);
- Adamu Lamuwa (Gombe);
- Mr. Innocent A. Iwejuo (Imo);
- M. S. Abubakar (Jigawa);
- Y. A. Ahmed (Jigawa);
- S. D. Umar (Kaduna);
- A. Sule (Kano);
- G. Y. Hamza (Kano).
- N. Rimi (Katsina);
- L. S. Ahmed-Remawa (Katsina);
- M. Manu (Kebbi);
- I. R. Ocheni (Kogi);
- I. A. Yusuf (Kogi);
- M. Abdulraheem (Kwara);
- W. A. Adedeji (Lagos);
- A. U. Ogah (Nasarawa);
- A. A. Musa (Niger);
- N. A. Kolo (Niger);
- S.O. Olaniyan (Ogun);
- A. R. Adejola (Ogun);
- O. E. Awe (Ondo);
- O. O. Aluko (Osun);
- I. A. Alatishe (Osun);
- V. A. Adeleke (Oyo);
- M. S. Adamu (Plateau);
- I. N. Charles (Rivers);
- Z. M. lfu (Taraba); da
- B. B. Hamman (Yobe).
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng