Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karbo bashin N850bn

Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karbo bashin N850bn

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta amince da bukatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na karbo bashin Naira Biliyan 850 domin bai wa gwamnatinsa damar aiwatar da kasafin kudin 2020.

A baya Majalisar Dattawa ta amince wa Buhari karbo bashin duk da cece kuce da ake yi game da karbo bashin.

Sai dai duk da hakan Majalisar Wakilan, a ranar Talata ta amince wa shugaban kasar karbo bashin cikin mintuna bakwai kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karbo bashin N850bn

Yanzu-yanzu: Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karbo bashin N850bn. Hoto daga The Punch
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje ya tsawaita dokar kulle a Kano

A wani labarin, kun ji cewa tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya a jamhiriyya ta uku wadda ta wakilci mazabar Makurdi da Guma, Cif Rebbeca Apedzan ta kamu da cutar coronavirus kamar yadda New Telegraph ta ruwaito.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar ta Benue zuwa uku.

Apezdan, wadda ta yi aiki a matsayin kwamishinan kasuwanci da masana'antu a lokacin mulkin Gwamna Goerge Akume a halin yanzu mamba ce a kwamitin amintattu na Hukumar Tattara Haraji na jihar, BIRS.

Gwamna Samuel Ortom ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai jim kadan bayan ganawa da kwamitin kar ta kwana na Covid 19 a gidan gwamnati a Makurdi.

Gwamnan ya ce ya yi cudanya da mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar a ranar Lahadi da ta gabata yayin wani taro duk da cewa ba su gwamutsu a wurin taron ba.

Amma duk da hakan ya yi alkawarin zai sake yin gwajin cutar ta Korona domin sanin matsayinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel