Babban Editan wata shahararriyar jarida ya rasa mahaifinsa a Kano

Babban Editan wata shahararriyar jarida ya rasa mahaifinsa a Kano

Mun samu labarin rasuwar Malam Miko Alhassan, mahaifin babban editan shahararriyar jaridar nan ta Daily Trust, Naziru Mika'ilu Abubakar.

Mallam Alhassan ya rasu yana da shekaru 89 a duniya kamar yadda mawallafan jaridar suka ruwaito.

Ya rasu ne a ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, bayan ya yi fama da wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da ta yi masa sababi na ajali.

Kamar yadda makusanta suka bayar da shaida, an haifi Malam Alhassan a garin Gora na karamar hukumar Madobi da ke jihar Kano a shekarar 1931.

Gabanin ajali ya katse masa hanzari, Malam Alhassan ya kasance daya daga cikin manyan dattawa na unguwar Koki da ke karkashin karamar hukumar cikin birni, inda ya yi rayuwa.

Ya rasu ya bar matarsa daya da kuma 'ya'ya 16. Mafi shahara cikin 'ya'yan da ya bari akwai babban editan jaridar Daily Trust wanda ya kasance tsohon edita a kafar watsa labarai ta BBC.

Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Asali: Twitter

Sai kuma Maikano Miko, mataimakin shugaba na cibiyar ci gaba da karatu kuma tsohon shugaban sashen kimiya na Physics a Kwalejin Ilimi ta Sa'adatu Rimi.

An jana'izarsa bisa koyarwa ta addinin Islama, kuma an binne shi a makabartar Kofar Mazugal da ke birnin Kano.

Haka kuma a jiya ne dai tsohon shugaban kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya NSE, Engr. Ibrahim Khaleel Inuwa, ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kano.

KARANTA KUMA: Masu sukar mu da yi wa dokar hana fita sakwa-sakwa ba su san komai ba a kan Kano - Ganduje

Tsohon shugaban NSE ya yi kacibus da ajali yana mai shekaru 71 a duniya.

Ya rasu ya bar mata daya da kuma 'ya'ya 9.

Hakika mutane da dama sun rasa rayukansu musamman a jihar Kano tun daga farkon watan Azumin Ramadana kawo yanzu.

Legit.ng ta ruwaito yadda masu hakar kabari a jihar Kano suka bayyana damuwa matuka kan yadda likafar yawan mace-mace ke ci gaba a jihar babu sassauci.

Mu na rokon Allah Madaukakin Sarki ya kyautata makwancin dukkanin wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Ya kuma sa Aljannah ce makoma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel