COVID-19: Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya ta kamu da korona

COVID-19: Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya ta kamu da korona

Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya a jamhiriyya ta uku wadda ta wakilci mazabar Makurdi da Guma, Cif Rebbeca Apedzan ta kamu da cutar coronavirus kamar yadda New Telegraph ta ruwaito.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar ta Benue zuwa uku.

Apezdan, wadda ta yi aiki a matsayin kwamishinan kasuwanci da masana'antu a lokacin mulkin Gwamna Goerge Akume a halin yanzu mamba ce a kwamitin amintattu na Hukumar Tattara Haraji na jihar, BIRS.

COVID-19: Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya ta kamu da korona
COVID-19: Tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya ta kamu da korona. Hoto daga Vanguard
Asali: Depositphotos

Gwamna Samuel Ortom ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai jim kadan bayan ganawa da kwamitin kar ta kwana na Covid 19 a gidan gwamnati a Makurdi.

DUBA WANNAN: Korona: Ta harbi karin mutum 242 a Najeriya, 64 a Kano, 49 a Katsina, 13 a Kaduna

Gwamnan ya ce ya yi cudanya da mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar a ranar Lahadi da ta gabata yayin wani taro duk da cewa ba su gwamutsu a wurin taron ba

Amma duk da hakan ya yi alkawarin zai sake yin gwajin cutar ta Korona domin sanin matsayinsa.

Ortom ya ce, "Na yi gwaji a baya, sakamakon ya nuna ban kamu ba amma na yi cudanya da ita Apedzan a ranar Lahadi. Mun halarci taro ni da ita duk da cewa ba mu gwamutsu wurin taron ba.

"Na umurci dukkan wadanda suka halarci taron da ni su zo ayi musu gwaji. Nima kai na zan sake yin gwajin domin a gano idan akwai wani abu. Zan sanar da mutanen jiha ta idan sakamakon ya fito."

A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnatin Jihar Kano ta sanar da tsawaita dokar kulle a jihar da sati daya a yunkurin ta na cigaba da yaki da annobar COVID-19 da aka fi sani da korona a jihar.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, wanda ya fitar da sanarwar ya ce an dauki matakin ne bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya da masu da tsaki a fanin lafiya.

Ya ce an dauki matakin ne domin rage yaduwar cutar tsakanin mutane ta hanyar cudanya wadda ke daya daga cikin hanyar da cutar ke yaduwa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar ta yi kira ga alummar jihar su kara hakuri tare da ba wa gwamnati goyon bayan a yakin da ta ke yi da annobar duk da irin halin da mutane ke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel