Annobar Coronavirus: Gwamnatin Gombe ta sanar da mutuwar mutum na farko

Annobar Coronavirus: Gwamnatin Gombe ta sanar da mutuwar mutum na farko

Gwamnatin jahar Gombe ta sanar da samun mutum na farko daya mutu a sakamakon mugunyar cutar nan ta Coronavirus mai sarke numfashin dan Adam a jahar.

Premium Times ta ruwaito shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na jahar, Idris Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da jawabi game da aikin kwamitinsu.

KU KARANTA: Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Fulani da Tibabe a Nassarawa, 5 sun mutu

Idris ya bayyana mamacin a matsayin dan shekara 50, wanda yace cutar ciwon siga na damunsa, kuma ya rasu ne da misalin karfe 4 na rana a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu.

Annobar Coronavirus: Gwamnatin Gombe ta sanar da mutuwar mutum na farko
Masu zanga zangar Corona a Gombe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mamacin ya boye rashin lafiyar dake damunsa, har sai da makwabcinsa ya kira kwamitin bayan ya fahimci ya na fama da matsanancin rashin lafiya bayan dawowarsa daga Bauchi.

Daga nan jami’ai suka dauki samfurin abubuwan da ake bukata don yin gwaje gwaje a tare da shi, wanda sakamakon ya nuna yana dauke da cutar, sai suka ka killace shi a asibitin Kwadon.

“Amma jikinsa ya kara tsananta a ranar Lahadi bayan rabin jikinsa ya mutu, hakan ta sa aka garzaya da shi zuwa sashin kula da wadanda ke matsanancin hali, watau COVID-19 ICU dake asibitin kwararru a Gombe, inda ya rasu da misalin karfe 4 na rana.” Inji shi.

Idris ya bayyana cewa jahar Gombe na da mutane 118 dake dauke da cutar Coronavirus daga gwaje gwaje 1,168 da suka gudanar.

A wani labarin kuma, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska dake rufe hanci da baki domin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Hadimin Ganduje a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sadarwar zamani ta Facebook a ranar Litinin, 11 ga watan Mayu.

Takunkumin wanda aka samar da su guda miliyan 2 tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jahar, za’a rabar da su ne a kananan hukumomin jahar guda 44.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng