Yanzu-yanzu: Har yanzu, Orji Uzor Kalu, na gidan yari

Yanzu-yanzu: Har yanzu, Orji Uzor Kalu, na gidan yari

- Har yanzu, bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, na daure a gidan yari duk da hukuncin kotu

- A ranar Juma'a, 8 ga Mayu, kotun kolin Najeriya ta yi watsi da hukuncin daurin shekaru 12 da aka yankewa Kalu na laifin rashawa

- A cewar rahoton, kotun bata ba da umurnin sakeshi bane saboda bai bukaci hakan ba

Duk da hukuncin kotun koli da tayi watsi da hukuncin daurin shekaru 12 da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, har yanzu yana tsare a gidan yari.

The Nation ta ruwaito cewa kotun bata bada umurnin sakeshi bane saboda Kalu bai bukaci hakan ba daga wajen kotun.

A cewar rahoton, Kwantrola Janar na hukumar gidaje gyaraa halin Najerya NCS, Ja'afar Ahmad, ya ki sakin Kalu saboda babu umurnin kotu cewa sakeshi.

An samu labarin cewa da yiwuwan Kalu ya garzaya kotun daukaka kara domin mika bukatan sakeshi.

KU KARANTA: Buhari ya bamu umurnin karbo maganin Koronan kasar Madagascar - SGF, Boss Mustapha

Kotun koli, a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu, ta soke hukuncin da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor-Kalu na shekaru 12 a gidan yari.

Kotun kolin, a wani hukunci da kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin Justis Amina Augie suka yanke, sun riki cewa babbar kotun tarayya ta Lagas ta yanke hukunci ba tare da hurumin yin hakan ba.

Wajen hukunta Kalu, da kamfaninsa na Slok Nigeria Limited da kuma tsohon daraktan kudi na jihar Abia, Jones Udeogu.

Ta riki cewa Justis Mohammed Liman wanda ya yanke hukuncin bai kasance alkalin babbar kotun tarayyar ba a lokacin da ya yi zaman yanke hukunci kan wadanda ake karar.

Ana zarginsu da satan kudi kimanin naira biliyan 1.7 daga asusun jihar Abia.

A cewar kotun kolin, Justis Liman bai da ikon dawowa ya zauna a matsayin alkalin babbar kotu kasancewar an dauke shi zuwa kotun daukaka kara kafin wannan lokacin.

Saboda haka, kotun kolin ta dage hukuncin da aka yankewa wadanda ake karan sannan ta yi umurnin sake sabon shari’a

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel