Tura ta kai bango: Jama'ar gari sun kashe 'yan bindiga 3, sun kama biyu a Zamfara

Tura ta kai bango: Jama'ar gari sun kashe 'yan bindiga 3, sun kama biyu a Zamfara

Jama'ar gari sun kashe mutum uku sun kuma mika wasu biyu ga sojoji a kauyen Karakkai a karamar hukumar Bungudu na jihar Zamfara.

Majiyar, Mallam Faruku Aliyu, ya sanar da jaridar The Punch cewa anyi bata kashi tsakanin yan bindigan da mutanen kauyen a daren ranar Jumaa inda yan garin suka yi nasarar kashe uku suka kuma kama biyu.

A cewar Faruku, yan bindigan sun iso kauyen ne domin su sace shanu amma sai mazauna garin suka fito kwansu da kwarkwata suka fi karfinsu.

Tura ta kai bango: Jama'ar gari sun kashe 'yan bindiga 3 sun kama biyu a Zamfara
Tura ta kai bango: Jama'ar gari sun kashe 'yan bindiga 3 sun kama biyu a Zamfara. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Dokar kulle: Limamai za su share gidan hakimi na sati daya a Kano

Sakataren hakimin Karakkai, Alhaji Mohammed Bashar, yayin da ya ke zantawa da majiyar Legit.ng a kan lamarin ya ce yan bindigan sun tafi kauyen ne da niyyar satar shanu amma yan garin suka hana su tafiya da shanun.

Ya yi bayanin cewa mutum biyu da aka kama kuma aka mika wa sojoji yan leken asiri ne a garin da suka saba kai wa yan bindigan bayani kan yadda za su gudanar da mummunar aikinsu.

Da aka tuntube shi a wayar tarho, mai magana da yawun Operation Hadarin Daji a jihar, Captain Ayo Oni-Orisan ya ce zai bincika ya ji kadin bayani kafin ya yi jawabi amma bai kira ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno zai kafa ofishi a kauyen Auno da ke karamar hukumar Konduga na jiharsa domin karfafa wa mutanen kauyen gwiwa da suka gudu saboda tsoron yan ta'adda su dawo gida.

A yayin da ya kai ziyara kauyen a ranar Asabar, Zulum ya ce zai rika amfani da ofishin daga lokaci zuwa lokaci domin karfafawa mutanen kauyen gwiwa su dawo gida.

Ya ce hakan na da muhimmanci sosai duba da kusancin da Auno ke da shi da babban birnin jihar da kuma Jami'ar jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya bukaci a kara samar da jamian tsaro a kauyen domin hakan zai karfafa wa mutane gwiwa.

Ya kuma umurci Ma'aikatar Sake Gina Garuruwa ta Tallafawa wadanda Iftilai ya fada musu ta yi gaggawar samar da abinci da kudi ga wadanda suke zaune a garin a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel