Yanzu-yanzu: Karo na biyu, masu cutar Korona suna zanga-zanga kan rashin kula

Yanzu-yanzu: Karo na biyu, masu cutar Korona suna zanga-zanga kan rashin kula

Kari na biyu cikin mako daya, masu fama da cutar Korona a jihar Gombe sun sake gudanar da zanga-zanga kan rashin kyakkyawawan kula da ake basu duk da suna killace.

A ranar Talata, Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda wasu mara lafiya a asibitin koyarwan dake Gombe da cibiyar killacewa dake karamar hukumar Yamaltu Deba suka yi zanga-zanga.

Yayinda ma-aikatan kiwon lafiyan jihar suka samu nasarar shawo kan lamarin masu cutar dake asibitin, sun gagara shawo kan wadanda ke Yamaltu Deba.

Sun cakudu da yan kauyen da suka tayasu yin zanga-zangar inda da yawa cikinsu suka ki dawowa cibiyar killacewan.

Wani mazaunin jihar da aka sakaye sunansa ya bayyanawa TheCable ranar Jumaa cewa abinda gwamnatin jihar tayi ya sa suka sake fitowa zanga-zanga yau.

Yanzu-yanzu: Karo na biyu, masu cutar Korona suna zanga-zanga kan rashin kula
Yanzu-yanzu: Karo na biyu, masu cutar Korona suna zanga-zanga kan rashin kula
Asali: Twitter

KU KARANTA EFCC ta yi martani a kan sakin Sanata Orji Kalu daga gidan yari

Yace “Bayan zanga-zangan ranar Talata, gwamnatin ta ji kunya, saboda haka ta mayar da hankali kan wadanda ke kwance a cibiyar killacewar garin Kwandon, inda ta manta da wadanda ke asibiti suna tunanin cewa jamian asibitin zasu iya kwantar da hankalinsu.”

Amma yayinda marasa lafiyan dake asibtin suka samu labarin cewa an inganta abubuwa a dayan wajen, sun fusata saboda sun ji gwamnati ta manta da su ne saboda basu yi zanga-zanga (kamar yadda na can sukayi ba.)”

”Saboda haka suke zanga-zanga a yau, suna tayar da hankulan mutane har sai lokacin da jamian tsaron suka samu nasarar tarwatsa su.”

Wata majiya a asibitin ta bayyanawa TheCable cewa wasu marasa lafiyan sun gudu gidajensu.

Kawo lokacin wallafa wannan rahoto, an nemi jin ta bakin kwamishanan lafiyan jihar, Ahmed Gana, amma yaki daukan wayarsa.

Za ku tuna cewa bisa kididdigan hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, akwai mutane 109 masu cutar Korona a jihar Gombe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel