Kano: Yadda aka yi min maganin korona – Shugaban kwamitin kar ta kwana

Kano: Yadda aka yi min maganin korona – Shugaban kwamitin kar ta kwana

Farfesa Abdulrazak Habib, Shugaba a kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a Kano, ya bayyana irin halin da ya shiga bayan kamuwa da korona da kuma yadda aka masa magani ya warke.

A ranar Alhamis 7 ga watan Mayu ne aka sallami Habib da wasu mambobin kwamitin na kar ta kwana da suka kamu da cutar tun ranar 17 ga watan Afrilu bayan sun warke.

Farfesan da ke aiki a Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano da Jamiar Bayero ya ce an bashi magunguna da yawa da suka hada da "ruwan magani da aka saka masa ta jijiyoyi, iskar oxygen da siracen habbatus sauda da aka rika shaka masa, shayin chitta da wasu abubuwan."

DUBA WANNAN: Ke duniya: An damke mutumin da ya birne mahaifiyarsa da ranta

An sanar da wannan bayanan ne a shafin Twitter na Ma'aikatar Lafiya na jihar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, "Ina farin cikin sanar da ku cewa an sallame ni daga cibiyar killace masu COVID-19 na Kano bayan gwajin da aka yi min ya nuna na warke kuma kusan dukkan alamomin cutar sun gushe.

"Na kamu da cutar ne lokacin da na ke aiki a kwamitin kar ta kwana na COVID-19 a jihar.

"Na yi fama da zazzabi, tari, sarkewar munfashi, amai, gudawa, mutuwar jiki, rashin iya cin abinci da sauransu. Na yi fama da ciwo na wata daya kuma an killace ni na kwanaki 20."

Ya jadadda cewa akwai bukatar maaikatan lafiya su wayar da kan mutane game da COVID-19 kuma su kiyayye dukkan sharrudan kare kai daga kamuwa daga cutar kamar guje wa cinkoso da amfani da takunkumin fuska.

Duk da cewa an sallami mutum 16 a suka warke a jihar a ranar Alhamis, an samu sabbin mutum 55 da suka kamu da cutar a ranar.

Hakan na nuna jimillar wadanda suke kamu da cutar a jihar ya kai 482 ciki har da 19 da suka warke da kuma 13 da suka mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel