Coronavirus: Bincike majalisar dinkin duniya ya nuna mutane 190,000 za su mutu a Afirka

Coronavirus: Bincike majalisar dinkin duniya ya nuna mutane 190,000 za su mutu a Afirka

Hukumar kiwon lafiya ta majalisar dinkin duniya, WHO. ta bayyana cewa mutane 190,000 daga nahiyar Afirka za su iya mutuwa a sakamakon annobar Coronavirus idan ba’a bi a hankali ba.

Premium Times ta ruwaito WHO ta bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da take gabatar da rahoton binciken da ta gudanar game da yaduwar annobar a yankin Afirka.

KU KARANTA: Alkalin da ya soke zaben Abiola na ranar June 12 1993 ya rasu a Bauchi

“Tsakanin mutane 83,000 zuwa 190,000 za su mutu a nahiyar Afirka daga cutar COVID-19, kuma tsakanin mutane miliyan 29 zuwa miliyan 44 za su kamu daga cutar a shekarar farko idan har ba’a dauki matakan dakatar da yaduwarta ba.” Inji ta.

Zuwa yanzu dai, alkalumman Worldometer sun nuna an samu mace mace 2,127 a Afirka, inda Egypt ke kan gaba da 495, Algeria 490 da Morocco 183, yayin da Najeriya ke da 100.

Coronavirus: Bincike majalisar dinkin duniya ya nuna mutane 190,000 za su mutu a Afirka
Shugaban WHO Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Binciken ya yi amfani da kasashen Afirka 47 tare da jimillan jama'ansu biliyan 1, inda ya nuna yaduwar cutar zai ragu, za’a samu karancin mace mace idan aka gwada da sauran kasashe.

“Hakan baya rasa nasaba da dalilai na yanayin muhalli da mu’amala wanda zasu yi sanadiyyar raguwar yaduwar cutar, tare da cewa yawancin matasan Afirka sun samu kariya daga cututtukan dake yaduwa kamar HIV da tarin fika, hakan zai rage yiwuwar kamuwarsu da cutar.

“Amma raguwar yaduwar cutar na nufin za’a dade cutar na ruruwa a nahiyar tsawon shekaru.”

Haka zalika binciken ta bayyana wasu kasashen Afirka dake cikin hadari idan suka yi wasa; Algeria, Afirka ta kudu da Kamaru.

Don haka WHO ta shawarci kasashen Afirka su fadada asibitocinsu musamman a matakin farko, kuma su tabbata sun samar da tsarin kula da masu neman agajin gaggawa.

Sa’annan ta shawarci kasashen Afirka su dage wajen yin gwaji, bin diddigi, killacewa tare da kulawa da masu cutar, idan kuma ba haka ba, za’a dade ana samun matsalar a yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel