Guzurin watan Ramadan: Illolin shan ruwan sanyi ga lafiyar dan Adam

Guzurin watan Ramadan: Illolin shan ruwan sanyi ga lafiyar dan Adam

Tabbas ruwan sanyi wani abu ne mai matukar sanyaya zuciya musamman ma a irin wannan lokacin da ake zabga tsabagen zafi.

Wannan ne ma yasa yawancin mutane idan sun fita sun sha rana ko kuma sun kai azumi, basu da wani buri da ya wuce su samu ruwan sanyin su su kwankwada.

1. TSAIDA BUGUN ZUCIYA: Bugun zuciya yana gyara dumin jiki da daidaita numfashi, to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa.

2. LALATA TSARIN KAYAN CIKI: Shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya, sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri, hakan ne ke janyo gyambon ciki (ulcer kenan).

3. TASHIN ZUCIYA: Masu shan ruwan sanyi a kai a kai za su rika yawan zubar da yawu da kaki, ko tashin zuciya, ko saurin kullewar ciki.

4. DAUKE KARFIN JIKI: Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi, amma a hankali yana dauke masa karfin jiki, saboda yayin da ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa, dole sai na'urorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin, hakan yanasa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi.

Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazzabi, a hankali kuma sai kuji ya daina.

Ruwan sanyi
Ruwan sanyi
Asali: UGC

5. CIWON MAKOGWARO DA DAKUSHEWAR MURYA:- Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro, har sukai ga basa amfaninsu.

Idan ya kai shekaru arba'in sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya, ko muryar ta fashe.

6. CIWON HANTA DA KODA:- Dukansu suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu, don haka yayin da mutum ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi, zai zamo su kuma suna cutuwa ta yadda aikinsu zai fara kasa, idan haka ta samu mutum ya shiga matsala.

7. BUSAR DA RUWAN JIKI:- Akwai na'urori a jikin dan Adam da aikinsu shine sadar da ruwa zuwa ko ina a jikin mutum, ta yadda ko ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi.

To wadannan naurorin sukan yi rauni sakamakon ruwan sanyi.

KARANTA KUMA: Rayuka 1.4m za su salwanta, mutane 6.3m za su kamu da tarin fuka saboda dokar kulle a kan cutar korona - Bincike

8. MATSALAR MA'AURATA:- Wannan abune tabbatacce harga likitocin zamani cewa: shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji, yana kuma busar da mace.

Shan ruwan sanyi:- Idan mahaifar mace nada rauni yana iya hana ta haihuwa.

Shan ruwan sanyi:- Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin inzali, ko kuma ya rage masa kuzari.

Shan ruwan sanyi:- Yana dauke ni'imar jiki mata da miji su zamo basa gamsuwa da junansu.

9. BASIR:- Shan ruwan sanyi tattare hanji yake, hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida, sai basir mai radadi (dankanoma) ya kama shi.

10. Ciwon barin kai (Migraine):- Wanda ke shan ruwan sanyi, gefen kansa zai rika ciwo, hakan yana kashe jijiyoyin ido a daina gani sosai, in yayi nisa har hauka yana sawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel