Ku daina zarginmu a kan cutar korona - China ta nuna wa Amurka yatsa
An ci gaba da musayar yawu gami da nuna yatsa a tsakanin kasar Amurka da ta China, dangane da surkullen da suka mamaye yanayin da ya haddasa barkewa cutar korona a duniya.
Gwamnatin Amurka na ci gaba da zargi da nuna yatsa a kan China, da cewar ita ta yi duk wani ruwa da tsaki na saken da ya janyo yaduwar annobar korona a duniya.
Sai dai gwamnatin China ta mayar martani tare da yiwa Amurka raddi da cewa, ba ta jin dadin wannan zargi da misalta a matsayin kazafi.
A ranar Alhamis ne dai gwamnatin China ta gargadi shugaban Amurka, Donald Trump, da cewa, ya gaggauta dawo wa daga rakiyar zarginta da kuma yi mata kage da ya saba.
Gwamnatin China ta misalta furucin Mista Trump a matsayin kalaman batanci, karya da kuma zantuka na shaci fadi da ba su da tushe.
A yayin ganawa da manema labarai, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar China, Hua Chunying, ta gargadi shugaban Amurka da ya daina zarginsu da sakacin barkewar annobar korona a duniya.
A makon da ya gabata ne Mista Trump ya sake nuna yatsa zuwa ga gwamnatin China, da cewa ita tayi sakacin da ya haifar da yaduwar cutar korona a duniya.
Kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito, Trump ya ce kasar China na da ikon hana yaduwar cutar zuwa sauran sassan duniya.
A hakan ne dai shugaban na Amurka ya ce tabbas sai an gudanar da gagarumin bincike domin gano matakan da gwamnatin China ta dauka tun a yayin da cutar korona ta fara bulla a kasar.
KARANTA KUMA: Coronavirus: Marasa lafiya sun tsere daga wuraren killace wa a jihohin Oyo, Bauchi da Neja
Mista Trump bai gushe ba dai yana ci gaba da cewa, kamata ya yi a ce gwamnatin China ta dauki matakai cikin hanzari na hana annobar korona bazuwa daga tushenta.
Babu shakka dai annobar coronavirus ta kashe dubban mutane a fadin duniya, tun bayan bullar bakuwar cutar mai shafar numfashi a Disamban 2019 cikin garin Wuhan na kasar China.
Haka kuma babu tantama a baya dai Shugaba Trump ya sha kiran cutar korona ''Yar China'.
Sakatarensa na harkokin waje Mike Pompeo yana kira cutar ''Yar Wuhan', abin da ke matukar bata wa gwamnatin China rai.
Trump da sakatarensa sun yi tir da gwamnatin China kan saken da ta yi daga farkon barkewar cutar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng