Yanzu-yanzu: Kwamishanan da Ganduje ya sallama kan isgilin mutuwar Abba Kyari ya kamu da Coronavirus

Yanzu-yanzu: Kwamishanan da Ganduje ya sallama kan isgilin mutuwar Abba Kyari ya kamu da Coronavirus

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa tsohon kwamishan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, ya kamu da cutar Coronavirus.

Muazu Magaji da kanshi ya bayyana hakan da safiyar Alhamis, 7 ga Mayu, 2020 a shafinsa na Facebook.

Yace: "Da safen nan sakamakon gwajin na na NCDC ya fito. An tabbatar da na kamu da cutar COVID-19 kuma an garzaya da ni daya daga cikin wuraren killace mutane. Ku tayamu addu'a."

Yanzu-yanzu: Kwamishanan da Ganduje ya sallama kan isgilin mutuwar Abba Kyari ya kamu da Coronavirus
Muazu Magaji
Asali: Facebook

Za ku tuna cewa a ranar 18 ga watan Afrilu, 2020, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya sallami kwamishinan ayyuka da gine-gine na jihar, Injiya Mu'azu Magaji.

Hakan ya biyo bayan mummunan furucin da yayi bayan mutuwar marigayi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Mai bada shawara na musamman ga Gwamna Ganduje ne ya wallafa hakan a shafinsa na Tiwita.

Legit.ng ta wallafa cewa, kwamishinan Ayyuka da Gine–Gine na jihar Kano, Muaz Magaji ya yi martani a kan rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari inda ya ce yanzu Najeriya ta samu yanci.

An rantsar da Magaji a matsayin kwamishina ne a ranar 5 ga watan Nuwamban 2O19

Ya yi wannan martanin ne a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Asabar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A baya kwamishinan ya taba wallafa wani rubutu inda ya yi fatan kada Abba Kyari ya dawo ya cigaba da ayyukansa a matsayin shugaban maaikatan fadar shugaban kasa bayan ya kamu da Covid-19 makonni kadan da suka gabata.

Kwamishinan ya yi kaurin suna wurin yin maganganu a kan alamura da suka shafi abokan adawarsa a siyasa a shafukan sada zumunta wadda hakan ke jan hankalin masu amfani da dandalin sada zumuntar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel