COVID-19: WHO ta kara samar da jami'ai 88 a Kano

COVID-19: WHO ta kara samar da jami'ai 88 a Kano

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta aike da Tawagar masu bayar da taimakon gaggawa, RRT, zuwa Kano domin tallafawa gwamnatin jihar dakile yaduwar COVID-19.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba cikin sanarwar da ta fitar inda ta ce hakan ya zama dole ne domin dakile yaduwar cutar a jihar cikin gaggawa.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa an samu bullar cutar a jihar a ranar 11 ga watan Afrilu ne amma a yanzu adadin wadanda suka kamu sun kai 342 kuma cutar ta kashe mutum takwas.

COVID-19: WHO ta kara samar da jami'ai 88 a Kano
COVID-19: WHO ta kara samar da jami'ai 88 a Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

A yunkurin ta na dakile yaduwar cutar, WHO ta sake aike wa da sabbin jami'ai masu sanya idanu 88 zuwa kananan hukumomi 44 da ke jihar.

A cewar WHO, jami'ai masu sanya idanun za su taimaka wurin kai rahoto game da wadanda ke da cutar da nemo wadanda suka yi cudanya da masu cutar da dakile yaduwar ta.

Jagoran tawagar WHO a jihar, Dr Jibrin Alkasim ya ce karuwar wadanda ke dauke da cutar a jihar ya sa dole a binciko wadanda suka yi cudanya da wanda aka gano suna da cutar.

Ya ce wadannan sabbin ma'aikatan da aka dauka za su taimaka wurin gano masu dauke da cutar a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu da kuma wadanda ke gidaje suna hulda da alumma.

Mr Alkasim ya ce wannan matakin da aka dauka zai taimaka wurin gano masu cutar da wuri tare da daukan mataki cikin gaggawa.

Ya ce, "Idan muna son samun kwararru da za su taimaka wurin yaki da COVID-19 musamman bangaren sanya idanu da wayar da kan mutane, ya zama dole mu horas da jamiai a kananan matakai."

Daya daga cikin wadanda aka bai wa horon, Muhammad Ibrahim ya ce: "Horaswar ya wayar mana da kai. Mun samu ilimi sosai a kan yadda za muyi yaki da annobar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel