Ministan Buhari, Raji Fashola ya bayyana matakin da yake dauka na kariya daga Coronavirus

Ministan Buhari, Raji Fashola ya bayyana matakin da yake dauka na kariya daga Coronavirus

Ministan ayyuka, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa ya kwashe tsawon kwanaki 49 ba tare da ya gaisa da kowa ba domin kare kansa daga annobar Coronavirus.

Fashola ya bayyana haka ne a ranar Talata, inda yace yayi hakan ne don dabbaka matakin kare kai da tsayawa nesa nesa da hukumar NCDC ta nemi a dabbaka don kare yaduwar cutar.

KU KARANTA: Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda

Ministan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda yace: “Yau kwana 49 rabon da na gaisa da wani. Dabbaka dokar tazara, sabon salo kenan, yaushe ka gaisa da wani.” Inji shi.

Kauce ma musabaha tare da wanke hannuwa a kai a kai na daga cikin dokokin kariya da hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fito da su don yaki da yaduwar cutar.

NCDC ta bayyana Legas a matsayin wanda ke kan gaba wajen yawan masu cutar, yayin da Kano ce ta biyu, Abuja, Borno, Gombe, Katsina da Ogun a matsayin jahohi biyar dake bin Kano.

Sanarwar ta ce an samu mutane; 43 a Legas, 32 a Kano, 14 a Zamfara, 10 a FCT, 9 a Katsina, 7 a Taraba, 6 a Borno, 6 a Ogun, 5 a Oyo, 3 a Edo, 3 a Kaduna, 3 a Bauchi, 2 a Adamawa, 2 a Gombe.

Yayin da jahohin Filato, Sakkwato da Kebbi ke da mutane 1 kowannensu. Wannan ne ya kawo jimillan masu cutar a Najeriya zuwa 2950, mutane 481 sun warke yayin da mutane 98 suka mutu.

A hannu guda kuma jahar Legas tana da mutane 1126 dake dauke da cutar, Kano 397, FCT Abuja 307, Borno 106, Gombe 98, Katsina 92, Ogun 91, Kaduna 84, Bauchi 83 sai Sakkwato ta goma 67.

A wani labarin kuma, a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu ne yan Najeriya daga jahohin Abuja, Legas da babban birnin tarayya suka fara fita bayan kwashe tsawon makonni 6 a garkame.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel