Serie A: Ronaldo da iyalansa sun koma kasar Italiya ana tsaka da annobar korona

Serie A: Ronaldo da iyalansa sun koma kasar Italiya ana tsaka da annobar korona

- Cristiano Ronaldo da iyalansa sun shiga birnin Turin na Italiya a cikin jerin gwanon motoci

- Dan shekaru 35 din zai killace kansa na kwanaki 14 don tabbatar da baya dauke da kwayoyin cutar korona

Shahararren dan wasan gaba na kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo, ya koma kasar Italiya yayin da ake daf da dawo wa domin karasa gasar Serie A nan ba da dade wa ba.

Ronaldo tare da iyalansa sun koma Italiya ne a wannan makon da muke ciki.

Tun a watan Maris, dan wasan mai shekaru 35 ya kasance a kasarsa ta Portugal inda ya ci gaba da yiwa dokar kulle da hana fita da'a saboda barkewar annobar korona a duniya.

A karon farkon bayan komawarsa gida, Ronaldo ya keɓe kansa na kwana 14 bayan da ya yi cudanya da daya daga cikin abokanan sana'arsa, Daniell Rugani, wanda cutar korona ta harba.

Bayan dawowarsa Italiya, dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar, an yi jigilarsa tun daga filin jirgin sama cikin jerin gwanon motoci zuwa farfajiyar da zai killace kansa na kwanaki 14.

Za a bai wa Ronaldao damar shiga cikin tawagar sauran 'yan wasan kungiyar Juventus bayan ya shafe tsawon makonni biyu a killace kuma kwararrun lafiya sun tabbatar ba ya dauke da cutar korona.

Kalli bidiyon rakiyar da aka yiwa Ronaldo bayan ya sauka a kasar Italiya:

Bayan iyalansa da ya dawo tare da su, an samu jami'an tsaro da suka yi rakiyarsa har gidansa da ke birnin Turin.

KARANTA KUMA: Yadda Gwamnatin Buhari za ta yi amfani da $311 da aka mayar wa Najeriya cikin kudin da Abacha ya sace

Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa, don tabbatar da tsaro sakamakon fargabar da ake yi wa cutar korona, Ronaldo bai samu damar shiga kasar Italiyan ba a ranar Litinin da ya kudirta, dalilan da suka sa aka jinkirta tafiyar zuwa washe gari.

Kungiyar Juventus wadda ake wa kirari da Old Lady, ta umurci dukkanin 'yan wasanta da su dawo sansaninta domin su ci gaba da horo da motsa jiki bayan samun amincewar gwamnatin Italiya.

Sai dai Ronaldo tamkar sauran 'yan wasan kungiyar, ba zai koma sansanin ba har sai an tabbatar ya tsarkaka daga cutar korona.

Kungiyar Juventus tana fatan ci gaba da jan ragama a saman teburin gasar Serie A ta bana, a yayin da kungiyar Lazio ta biyo bayanta da banbancin maki daya kacal a tsakaninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel