'Yan bindiga sun kashe mutum daya, sunyi garkuwa da wasu da dama a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutum daya, sunyi garkuwa da wasu da dama a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe wani mai gadi, sun kuma sace wasu mutane uku a Kaduna ciki har da wani ma'aikacin banki, Sarkin Doka da diyarsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a unguwannin Danhono II da Dokan Mai Jamaa da ke Millenium City a karamar hukumar Chikun na jihar.

Harin da aka kai a daren ranar Litinin misalin karfe 9 na dare shine makamancinsa na hudu da aka kai a unguwar cikin wata daya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa yan bindigan sun kashe mai gadin, Emmanuel a lokacin da suka yi nasarar kutsa wa gidan ma'aikacin bankin.

'Yan bindiga sun tafka ta'adi a wasu unguwanni a Kaduna

'Yan bindiga sun tafka ta'adi a wasu unguwanni a Kaduna. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Tuni da babban kwamandan hedkwatan sojoji ta 1 Division da kwamishinan tsaron na jihar sun ziyarci unguwannin da abin ya faru.

Wata majiya daga Doka da ta ce sunan ta Peace ta ce, "Abin ban tsaro ne. Misalin karfe 9 na dare ne bayan mutane sun kwanta sai muka fara jin karar harbin bindiga.

"Da farko munyi tsamanin yan banga ne ke harbi amma daga baya muka gano cewa yan bindiga ne suka kawo hari a unguwar.

"Sun kashe mai gadi sannan sun sace wasu mutane uku ciki har da Sarki. Mun gano cewa sun kai hari Danhono II sun kuma sace wani ma'aikacin banki da diyarsa."

"Mun gano cewa sun kuma tafi wasu unguwannin biyu sun sake sace wasu mutane biyu bayan yin musayar wuta da sojoji."

Da ya ke yabawa yan sanda saboda amsa kira cikin gaggawa, ya ce,"Lokacin da abin ya faru, mun kira yan sanda kuma sun amsa nan take, duk da cewa ba su ceto wadanda aka sace ba, sun girke motocinsu biyu a unguwar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel