Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa mahaifiyar Buratai rasuwa a Borno

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa mahaifiyar Buratai rasuwa a Borno

Allah ya yi wa Kakah Hajja, mahaifiyar babban hafsin sojojin Najeriya rasuwa a ranar Talata.

Wata majiya daga dangin su Buratai ya shaida wa Sahara Reporters cewa marigayiya Hajja ta rasu ne bayan tayi fama da gajeruwar rashin lafiya a gidan ta da ke Maiduguri a jihar Borno.

Majiyar ta ce, "Eh, tabbas ina tabbatar muku da cewa ta rasu.

"Ta rasu da yammacin yau kuma za a yi mata janaiza gobe da karfe takwas na safe.

"Allah ya jikan ta da rahama. Amin."

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa mahaifiyar Buratai rasuwa a Borno
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa mahaifiyar Buratai rasuwa a Borno. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Gwanda da akuya ‘sun kamu’ da COVID-19 a Tanzania

A wani rahoton, mun kawo muku cewa Allah ya yi wa dan majalisar jihar Borno, Umar Audi rasuwa

Wata majiya daga asibitin ta ce da farko ba a karbi Audi ba saboda babu gado.

An ce ma'aikatan lafiya a asibitin sun dage cewa babu gadon da za a bashi inda suka ce gadon kawai da ya rage na mata masu haihuwa ne.

Amma iyalansa da suka kai shi asibitin sunyi kokarin shawo kan ma'aikatan asibitin inda daga bisani suka karbe shi.

Majiyar ta ce, "Ya mutu jim kadan bayan an bashi gado. An dauki samfuri daga jikinsa an aike wa Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa, NCDC, domin a tabbatar idan mutuwarsa na da alaka da COVID-19.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel