Abubuwa 10 da za a rika tuna Yar’adua da su

Abubuwa 10 da za a rika tuna Yar’adua da su

A rana mai kaman ta yau ne, 5 ga watan Mayu, amma shekaru goma da suka gabata ne tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’ Adua ya rasu a kan mulki.

Duk da cewa shekaru uku kawai ya yi a kan mulki gwamnatinsa ta dukufa wurin aiwatar da wasu ayyuka da tsare tsare inda wasu daga cikinsu an kammala su.

Ga dai jerin wasu abubuwa goma da za a rika tuna tsohon shugaban kasar da su kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa:

Abubuwa 10 da za rika tuna Yar’adua da su
Abubuwa 10 da za rika tuna Yar’adua da su. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

1. Sakin kudaden kananan hukumomin jihar Legas

Ba za a taba mantawa da marigayi Shugaba Yaradua ba domin shine ya bayar da umurnin sakin kudaden kananan hukumomin jihar Legas ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rike inda ya nuna kin amincewarsa a kirkirar Hukumar Cigaban Kananan Hukumomi (LCDA).

Gwamnatin Obasanjo ta ki sakin kudaden duk da cewa kotu ta bayar da umurnin hakan.

DUBA WANNAN: Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10

2. Kirkirar shirin Afuwa da talllafi ga tsageran Neja Delta

Yaradua ya kawo zaman lafiya a yankin Neja Delta ta shirinsa na yin afuwa ga tsegerun yankin muddin za su ajiye makamai.

Masu tayar da kayan bayan sun yi amfani da damar da ya basu sun ajiye makamansu.

Wannan abin ya yi sanadin samun cigaba a bangaren samar da man fetur da iskar gas a kasar.

Hakan ne kuma ya yi sanadin kirkirar Maaikatar Neja Delta.

3. Bayyana kadarori

A ranar 28 ga watn Yunin 2007, Yar’Adua ya bayyana wa duniya kadarorin da ya mallaka, shine shugaban kasa na farko da ya fara yin hakan a tarihin kasar.

A lokacin ya bayyana cewa ya mallaki kadarorin da suka kai ₦856,452,892 ciki Naira Miliyan 19 na matarsa ne.

Ya kuma bayyana cewa ana bin sa bashi na ₦88,793,269.77.

4. Bin dokokin kasa da biyayya ga hukuncin kotu

A zamanin da ya ke mulki, ana yi wa marigayi Yaradua lakabi da "Mr Rule of Law" wato mai biyayya ga doka saboda mutunta hukuncin kotu da ya ke yi.

A zamanin mulkinsa Jamiyyar People’s Democratic Party (PDP) mai mulki da rasa jihohi kamar Edo, Ondo, da Osun a kotu.

5. Kyakyawan alaka tsakanin bangaren zartarwa da bangaren masu yin doka

Daya daga cikin abubuwan da za a rika tuna marigayi Yaradua da shi shine rashin yi wa juna katsalandan tsakanin bangaren zartarwa da masu yin doka.

Wannan shine dalilin da yasa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taba cewa marigayi Shugaba Yaradua dan siyasa ne da a zamaninsa ba samu rikici ba tsakanin bangaren masu yin doka da masu zartarwa.

6. Kwamitin yi wa dokokin zabe garambawul na Justice Mohammed Lawal Uwais

Za kuma a rika tuna gwamnatinsa saboda kafa kwamitin Justice Mohammed Lawal Uwais na yin gyar ga dokokin zabe da za su taimakawa yadda ake gudanar da zabe a kasar idan an aiwatar da shawarwarin.

7. Seven-Point-Agenda

A ranar 1 ga watan Augustan 2007, gwamnatin Yaradua ta sanar da wasu bangarori bakwai da za ta mayar da hankali a kai da suka da da Makamashi da lantarki, Samar da abinci, Yalwata arziki a kasa, Inganta Sufuri, Sauye sauye a bangaren filaye, Inganta tsaro da Ilimi.

8. Sauyi a kundin tsarin mulkin PDP domin kwace shugabancin kwamitin amintattu daga hannun tsaffin shugaban kasa

Shi ne ya jagoranci yi wa kundin tsarin mulkin jamiyyar PDP garambawul ta yadda aka tsige tsohon shugaban kasa Oluesegun Obasanjo a matsayin shugaban kwamitin amintattu na jamiyyar.

9. Fadada manyan titunan Kubwa da na Airport road

Gwamnatin tsohon shugaban kasa Yaradua ne ta samar da kudaden da aka yi amfani da su wurin fadada titin Kubwa da na Airport road da aka karasa aikin a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

An sauya sunan Airport road zuwa maru Musa Yar’adua Expressway bayan kammala aikin.

10. Fadada Rafin Niger

Gwamnatin marigayi Yaradua ta mayar da hankali sosai wurin aikin fadada Rafin Niger amma anyi watsi da aikin bayan rasuwarsa.

Rafin Niger yana da matukar muhimmanci wurin inganta kasuwanci da tattalin arzikin arewacin Najeriya duba da cewa rafin ne zai hada kudanci da arewacin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164