Allah ya yi wa Sarkin Kauran Namoda rasuwa

Allah ya yi wa Sarkin Kauran Namoda rasuwa

Sarkin Kiyawan Kauran Namoda a jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Ahmad Asha ya rasu.

Sarkin ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2020 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda wani na kusa da fadar sarkin ya tabbatar wa BBC.

Ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, ya kuma bar mata uku da yaya da dama.

A halin yanzu babu wani cikakken bayani game da abinda ya yi sanadin rasuwarsa.

Sarkin ya rasu bayan shafe shekaru 16 a gadon sarauta.

Allah ya yi wa Sarkin Kauran Namoda rasuwa
Allah ya yi wa Sarkin Kauran Namoda rasuwa. Hoto daga BBC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje ya sassauta dokar kulle a Kano, ya sanar da ranakun walwala

Marigayi Ahmad Asha ne sarki na biyu a tarihin sarautar Sarki mai sanda mai daraja ta daya a Kauran na Namoda bayan mahaifinsa, amma shine Sarki na 16 a jerin sarakunan masarautar Kiyawan Kauran Namoda.

A wani labari mai kama da wannan, kun ji cewa Allah ya yi wa sarkin Rano ta jihar Kano, Alhaji Tafida Abubakar II rasuwa.

Sarkin wanda ake kira da Autan Bawo, ya rasu ne a ranar Asabar yana da shekaru 74 a duniya.

Turakin Rano kuma dan majalisar mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, Alhaji Alhassan Rurum ne ya tabbatar da wannan babban rashin ga jaridar Solacebase.

Kamar yadda ya bayyana, za a birne marigayin basaraken ne da yammacin ranar Asabar a masarautarsa.

Marigayin sarkin ya rasu ya bar yara 17 da kuma mata biyu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an kwantar da Sarkin a asibiti a ranar Juma'a bayan rashin lafiyar da ya kwanta.

An gano cewa an hanzarta mika Sarkin asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano.

A cikin halin tsanantar rashin lafiyar, an mayar da shi asibitin kwararrun da ke Nasarawa don ci gaba da samun kulawar masana kiwon lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel