Gwamnatin jiha ta bayyana cututtuka biyu da ke kashe mutane a Kano

Gwamnatin jiha ta bayyana cututtuka biyu da ke kashe mutane a Kano

Gwamnatin jihar Kano a ranar Juma'a ta ce binciken da aka fara gudanarwa a kan mace macen da aka samu a jihar ya nuna cewa mafi yawa cikin wadanda suka mutu zazabin cizon sauro ne da sankarau suka kashe su.

Mafi yawa daga cikin su suna da wasu cututtuka da suke fama da su kamar hawan jini, ciwon suga da wasu cututtukan a cewar wakilin gwamnatin jihar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun gwamna Ganduje, Salihu Yakasai ya cewa galibin wadanda suka mutu ba su samu kulawan likitoci ba kafin suka mutu.

Gwamnatin jihar tare da hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, da Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Afirka da ta Najeriya, NDCD, suna bincike don gano abinda ya yi sanadin mace macen da wasu ke dangantawa da COVID-19.

Kano:Sankarau da zazabin ciwon sauro ke kashe mutane ba korona ba
Kano:Sankarau da zazabin ciwon sauro ke kashe mutane ba korona ba. Hoto daga Observers Times
Asali: UGC

DUBA WANNAN Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu

Mista Yakasai ya shaidawa gidan rediyon DW Hausa a ranar Jumaa cewa majinyatan da ke fama da wasu cututtukan "sun mutu ne don ba su samu kulawa daga asibitocin gwamnati da masu zaman kansu ba a lokacin ana fargabar COVID-19."

Ya kuma ce mafi yawancin asibitoci masu zaman kansu a jihar ba su aiki saboda annobar ta korona.

Akwai yiwuwar wannan ya shima yana daga cikin dalilan da yasa aka samu mace macen da yawa a jihar. Ya ce gwamnan jihar ya gana da masu asibitoci masu zaman kansu a kan batun.

Ya kuma bayyana cewa mambobi hudu na kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a jihar sun kamu da coronavirus.

Amma ya nuna rashin jin dadinsa yadda wasu mutane ke izgili game da lamarin da ya ce hakan na iya kawo koma baya cikin yaki da cutar da ake yi a jihar.

Ya ce ma'aikatan lafiya suna bukatar yabo ne da goyon baya ba cin mutunci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel