Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEMA

Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEMA

– Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa NEMA

– Sabon shugaban da aka nada shine AVM Muhamadu Alhaji Muhammed (Mai ritaya) wanda zai yi aiki na shekaru hudu

– AVM Muhamadu Alhaji Muhammed (mai ritaya) zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar, Injiniya Mustaha Y. Maihaja

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin AVM Muhamadu Alhaji Muhammed (Mai ritaya), a matsayin sabon shugaban Hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa (NEMA).

Nadin da aka yi wa Muhammed zai fara aiki ne daga ranar Alhamis 30, ga watan Afrilun 2020 inda zai karbi ragamar mulkin hukumar daga tsohon shugaban ta Injiniya Mustaha Y. Maihaja.

Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEMA
Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEMA. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu

A cewar sanarwar da Direktan watsa labarai na Ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mista Wille Bassey ya fitar a yammacin ranar Asabar, Muhammad zai yi aiki na waadin farko na tsawon shekaru hudu.

Sanawar ta ce, "Nadin za ta fara aiki daga ranar Alhamis 30, ga watan Afrilun 2020 na waadin farko na shekaru hudu kamar yadda sashi na 3 na Dokar National Emergency Management Agency Act ta tanada.

"An umurci tsohon shugaban hukumar mai barin gado, Injiniya Mustaha Y. Maihaja ya mika dukkan takardu da bayyanai na ayyuka ga AVM Muhammadu Alhaji Muhammed (Mai ritaya)nan take.

"Shugaban kasar kuma ya mika godiyarsa da shugaban hukumar mai barin gado kana ya bukaci sabon shugaban ya yi aiki tukuru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel