Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Rano rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Rano rasuwa

- Allah ya yi wa sarkin Rano na jihar Kano, Alhaji Tafida Abubakar II rasuwa a yau Asabar

- Sarkin, wanda aka sani da Autan Bawo ya rasu yana da shekaru 74 kuma ya bar 'ya'ya 17

- Turakin Rano, Alhaji Alhassan Rurum ne ya tabbatar da rasuwarsa ga jaridar Solacebase

Allah ya yi wa sarkin Rano ta jihar Kano, Alhaji Tafida Abubakar II rasuwa.

Sarkin wanda ake kira da Autan Bawo, ya rasu ne a yau Asabar yana da shekaru 74 a duniya.

Turakin Rano kuma dan majalisar mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, Alhaji Alhassan Rurum ne ya tabbatar da wannan babban rashin ga jaridar Solacebase.

Kamar yadda ya bayyana, za a birne marigayin basaraken ne da yammacin yau Asabar a masarautarsa.

Marigayin sarkin ya rasu ya bar yara 17 da kuma mata biyu.

Allah ya gafarta masa ya kyautata tamu.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Rano rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Rano rasuwa. Hoto daga HausaAll
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an kwantar da Sarkin a asibiti a ranar Juma'a bayan rashin lafiyar da ya kwanta.

An gano cewa an hanzarta mika Sarkin asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano.

A cikin halin tsanantar rashin lafiyar, an mayar da shi asibitin kwararrun da ke Nasarawa don ci gaba da samun kulawar masana kiwon lafiya.

Karin bayani na nan tafe...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel