Kano: An kwantar da Sarkin Rano a asibiti

Kano: An kwantar da Sarkin Rano a asibiti

Sarkin Rano, Dr Tafida Abubakar IIa II, daya daga cikin sabbin sarakunan masarautu hudu da aka kirkira a Kano yana asibiti a kwance kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai ba a tabbatar ko rashin lafiyar sarkin na da nasaba da annobar Covid-19 ba.

Wata majiya daga Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano (AKTH) ta sanar da Daily Trust cewa an kawo mai martaba Dr IIa II asibitin a safiyar yau cikin alamun da ke nuna rashin lafiyar ta yi tsanani.

Majiya ta kuma sai an tura Sarkin Asibitin Kwararru na da ke Nassarawa domin cigaba da bashi kulawa.

Kano: An kwantar da Sarkin Rano a asibiti

Kano: An kwantar da Sarkin Rano a asibiti. Hoto daga Daily Trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Cutar Korona ta sake kashe wani babban mutum a Kano

"A halin yanzu da na ke magana da kai (misalin karfe 2.55 na rana), motar da za ta tafi da sarki zuwa asibitin Nassarawa ta bar harabar AKTH. Jikin sarkin ya yi tsanani a lokacin da suka bar AKTH," in ji majiyar.

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, wani mai rike da sarautar gargajiya a masarautar Rano da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ta farko an garzaya da sarkin zuwa AKTH amma saboda babu iskar Oxygen sai aka tura shi zuwa Asibitin Nassarawa.

Ya ce, "Bisa ga dukkan alamu ciwon da ke damun sarkin ya yi tsanani, tana iya yiwuwa COVID-19. Allah dai ya kiyaye mu baki daya, amma abin ban tsaro ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel