Majalisar zartarwa ta fidda sunayen mutane 9 da suka cancanci cin gajiyar mukamin Abba Kyari

Majalisar zartarwa ta fidda sunayen mutane 9 da suka cancanci cin gajiyar mukamin Abba Kyari

A yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan wanda zai zamo sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, 'yan majalisar zartarwa na neman a zabi daya daga cikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa, yan majalisar zartarwa na neman a nada daya daga cikinsu a matsayin wanda zai ci gajiyar kujerar marigayi Abba Kyari.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wasu daga ministoci kasar da ke neman a nada daya daga cikinsu, sun daura damarar gamsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya amince da kudirinsu.

'Yan majalisar zartarwar na ganin a cikinsu akwai wadanda ke da cancanta ta dora wa daga inda tsohon shugaban ma'aikatar fadan shugaban ya tsaya da aiki bayan ya kwanta dama.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, marigayi Kyari wanda ake gani a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Najeriya mafi girman tasiri da kuma iko a tarihin kasar nan, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu.

Ajali ya katse hanzarin Mallam Kyari a asibitin First Consultants da ke garin Ikoyin jihar Legas bayan ya sha fama da cutar korona inda ya yi jinya ta tsawon makonni.

Shugaba Buhari tare da marigayi Abba Kyari
Shugaba Buhari tare da marigayi Abba Kyari
Asali: UGC

A bisa tsari da kuma koyarwar addinin Islama, an binne gawar marigayi Kyari cikin zubar hawaye ta 'yan uwa da makusanta a ranar Asabar, 18 ga Afrilu, a makabartar dakarun soji ta Gudu da ke garin Abuja.

Mutuwar kwararren a kan nazarin shari'a da doka wanda kuma ya shiga siyasa dumu-dumu, ta bar makeken tabo a zukatan iyalansa da dangi da kuma masoya.

KARANTA KUMA: A kwana 2 an samu masu cutar korona 118 a jihar Kano - NCDC

Haka zalika mutuwar Kyari wanda ya kasance dan asalin jihar Borno, ta bar babban gibi a gwamnatin shugaban kasa Buhari wanda ya yi tasirin gaske a cikinta yayin jagorancinsa.

Ana ganin da yawa daga cikin manya a Najeriya sun cancanci maye gurbin marigayi Kyari musamman tsohon ministan harkokin waje, Babagana Kingibe, wanda ake gani bajimi ne cikin 'yan siyasa a kasar.

Yayin da aka yi nisa cikin tattaunawa kan wanda zai zamo shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ministocin Buhari na son a zabi macancanci daya daga cikin majalisarsu ta zartarwa domin tabbatar da gudanar hadin kai da amininci a tsakaninsu kamar yadda ta kasance da marigayi Kyari.

Sunayen mutum 9 da majalisar da gabatar wa da Buhari sunayensu sun hadar da;

1. Adamu Adamu (Ministan Ilimi)

2. Boss Mustapha ( Sakataren gwamnatin tarayya)

3. Suleiman Adamu (Ministan Ruwa)

4. Sen. Hadi Sirika (Ministan Sufurin jiragen sama )

5. Ya’u Shehu Darazo (Babban haidmin shugaban kasa kan harkoki na musamman)

6. Abubakar Malami (Ministan Shari'a kuma Lauyan kolu na kasa)

7. Sadiya Umar Farouq (Ministar Agaji da Ci Gaban Al'umma)

8. Rotimi Amaechi (Ministan Sufuri)

9. Babatunde Raji Fashola (Ministan Ayyuka da Gidaje).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel